Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya bukaci yan Najeriya su zama tsintsiya madaurin ki daya da cigaba da imani da dunkulewar kasar nan domin samun cigaban ta.
A sakon sa, Lawan ya taya yan Najeriya bikin cika 61 da samun yancin kan kasar nan.
Yace, "abin jin dadi ne da muka ga dorewar dimokaradiyya mafi dadewa a tarihin mu a matsayin kasa
Bayanin hakan, na kunshe ne a wata takardar manema da mai baiwa shugaban shawara akan aikin jarida, Ola Awoniyi ya fitar a yammacin juma'ar makon nan da ake bukin yancin Najeriya.
"Ana iya ma wannan nasara kallon karama amma kuma wanj karin dalili ne da za mu yi murna da shi ne idan aka yi la'akari da tarihin zamantakewar mu.
"A ko da yaushe duk dan kishin kasa zai alfaharin tunawa da lokaci mai dimbin tarihi a ranar daya ga watan Oktoba na shekarar 1960 da aka saukar da tutar kasar Ingila aka maye ta da mai launin girin da fara da girin.
"Wannan ya nuna mana cin ma burinmu na samun yanci daga mulkin mallaka na turawa. Shine kuma farkon fara gina dukulalliyar kasa cikin zaman lafiya da walwala.
"Shugabannin mu na baya sun fuskanci wahaloli ta dalilin bambance-bambancen da ke tsakanin mu. Sai dai sun fahimci ba mu kadai ne ke da irin wannan bambance-bambancen ba a don haka suka rungume su a matsayin wata hanya ta karfafa kasar nan.
"Kalubalen da muke fuskanta a yau suna da dama amma ana iya shawo kan su. Hakika masu zuwa a bayan mu zasu tuna da mu idan muka fuskanci wadannan kalubalen kamar yadda shugabannin mu na baya suka fuskanci nasu kalubalen.
"Akwai bukatar shugabannin mu na siyasa da addini da sarakunan gargajiya da ma masu fadi aji a kasar ma su hada kan su domin cigaban kasar mu.
"Ya kamata a duk lokacin da wata matsala ta taso muyi amfani da hanyar da ta kamata wajen warware ta. Najeriya kasa ce ta dukkan mu ba tare da wani fifiko ba.
"Don haka nike kara bukatar dukkan yan Najeriya da su dauki damar da yunkurin da majalisar dokoki ta tarayya ta ke yi a yanzu haka na gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan.
"Majalisar ta sha alwashin tabbatar da yin gyara mai amfani ga kundin tsarin mulkin kasar nan don tabbatar da cewa kundin tsarin mulkin ya cigaba da amfanar da yan kasa.
"Kundin tsarin mulki zai cigaba da warware matsalolin da muke fuskanta, a wannan dalilin ne majalisar dokoki ta tarayya ta ba aikin muhimmanci.
"Mu cigaba da yin imani da Najeriya da cigaba da zama al'umma daya don yi aiki tare saboda samar da tsaro da walwala. Allah ya albarkaci Najeriya".