Bukin Sallah: Talakawa Sun  Nuna Goyon Bayansu Ga Sarkin Kagara

Bukin Sallah: Talakawa Sun  Nuna Goyon Bayansu Ga Sarkin Kagara

 

 

Daga Awwal Umar Kontagora, a Kagara

 

 

A karon farko, masarautar Kagara ta jihar Neja ta shirya bukin hawan sallah wanda irin shi ne farko a masarautar bisa jagorancin mai martaba Malam Ahmed Garba Attahiru Gunna II, bukin wanda ya kayatar kuma ya samu karbuwa a wajen talakawa inda suka nuna goyon bayan su ga sarkin bayan fitowarsu kwai da kwarkwata har da matasa, matan aure da tsoffi da yan mata da yin jinjina da nuna goyon bayan su ga sabbin tsare-tsaren da sarkin ya kawo dan nuna tsantsagerarriyar al'adar masarautun Hausa.

Tunda farko a ranar littinin da aka gabatar da sallar Idi a masallacin Idi inda dukkanin hakimai da dagattai da masu rike da sarautu a masarautar da talakawa suka halarci sallar Idi duk da matsalolin rashin tsaro da masarautar ta fuskanta a baya.

Mai martaba sarki, Malam Ahmad Gunna da hadin guiwar gwamnati da jami'an tsaro sun taka rawar gani wajen dawo da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a, inda aka tabbatar da an samar da tsaro a dukkan kusurwowin masarautar ta yadda walwala da jin dadin jama'a ya sake samun tagomashi.

A bayaninsa, bayan kammala sallar Idin bisa hawa na kasaita irin ta sarakuna da ya gudana a farfajiyar fadar sarkin, mai martaba ya jawo hankalin jama'a wajen cigaba da baiwa masarautar goyon baya, tare da cire duk wani bambance bambancen da ke tsakanin su na siyasa, kabila da jinsi dan cigaban masarautar.

Mai martaba, Malam Ahmad Garba Attahiru na II, ya baiwa al'ummar masarautar tabbacin zai yi iyakacin kokarinsa wajen tabbatar da hadin kai, gina kasa, cigaban harkokin noma da kiwo wanda shi ne zai cigaba da bunkasa tattalin arzikin al'umma, karamar hukumar Rafi, jiha da kasa baki daya.

A tsokaninsa, Tambarin Kagara, Hon. Danladi Umar Abdulhamid, yace sabbin tsare-tsaren da sarki ya kawo daidai suke da koyarwar addini, wanda hakan zai zamo silar dawo da zaman lafiya, tsaro da cigaban masarautar.

Abdulhamid, ya cigaba da cewar irin salon mai martaba na tafiyar da sarautar kasar Kagara abu ne da zai gamsar da kowa da nuna irin kwarewarsa ga mulkin masarautar a zamanance da kuma tsari irin na al'ada.

Alhaji Sahabuddin Isah, Tafidan Kagara kuma tsohon shugaban riko na karamar hukumar Rafi, yace yanzu masarautar Kagara daidai take da dukkanin masarautun Arewacin kasar nan, bisa natija da kwazo da kokarin hada kan al'ummarta.

A kokarinsa na dawo da martabar masarautar, mai martaba ya shirya hawan daushe irinsa na farko da saduwa da talakawa inda yayi fita irin ta kasaita ya zagaya cikin garin Kagara, dan karban gaisuwar sallah ga talakawa, inda suka fito lungu da sako dan nuna mubayi'arsu ga sarkin talatar makon nan, sarkin ya samu karbuwa ta hanyar yin kwalliya da fitowa dan karban goron sallah, mai martaba ya nuna farin cikinsa ganin irin yadda talakawa suka karbe shi hannu biyu tare da nuna farin ciki, guda da raye-raye irin ta al'ada.

Malam Ibrahim Balarabe, Santurakin Kagara, kuma wakilin gwamnatin jiha, yace gwamnati a shirye take wajen samar da dukkanin abubuwan more rayuwa ga al'ummar masarautar.

Ya cigaba da cewar bisa jajircewar mai martaba sarki, yanzu haka gwamnatin jiha na yunkurin gyara babban asibitin gwamnati da ke Kagara, makarantar sakandare ta farko da ya shiga cikin tarihi wanda ya yaye dubban mutane da kasar nan ke alfahari da su, ba dan komai ba sai a yunkurin gwamnatin jiha na tabbatar kowace masarauta ta anfana da mulkin dimukuradiyya.

Santuraki, ya jawo hankalin yan siyasa musamman ganin babban zabe na karatowa a kasar nan, da su cire bambancin jam'iyya, domin koda yan takara dubu suka fito mutum daya ne dai zai samu nasara, su tabbatar sun hada kai wajen ganin cigaban zaman lafiya a kasar Rafi.

Tabbas, duniya ta shaida irin sauye-sauyen da aka samu a masarautar Kagara, sauyi ne da duk mai sha'awar cigaba zai yi na'am da shi. Domin bayan sake fasalin masarautar, da tsare-tsaren masarautu na wannan masarauta, mai martaba a matsayin shi na kwararre kuma mai ilimi ya dukufa wajen ganin masarautar ba a barta a baya, ta fuskar cigaba da inganta rayuwar talakawa.

Kan matsalar tsaro da muka fuskanta a baya, gwamnati da jami'an tsaro, sun dukufa ba dare, ba rana na ganin ta kawo karshe ta'adda da ta'addanci a jihar nan.

Matsalar tsaro ba jihar nan kawai ba ne, matsala ce da ta shafi kasa baki daya, wanda kuma gwamnati ta tabbatar ba za ta runtsa ba saboda irin matakan da take dauka, har sai ta murkushe yan ta'adda a kasar nan.

Hon. Isma'ila Modibbo, shugaban karamar hukumar Rafi, ya jawo hankalin matasa da su daina barin baragurbi na anfani da su da sunan bangar siyasa, gwamnatinsa ta kawo tsare-tsaren da matasa zasu anfana ta hanyar dogaro da kai.

Yace " Ina kira da babban murya ga yan uwana yan siyasa da mu ji tsoron Allah, mu ajiye bambancin siyasa, jam'iyya ya zamanto kasar Rafi ne farko a zukatan mu ba kawunan mu ba, yanzu mun samu nagartaccen uba da yazo tarbiyartar da mu soyayya, kauna da hadin kai, domin na yaba da irin matakan da mai martaba ke dauka na cigaban kasar Kagara.

Mai martaba sarki, Malam Ahmad Garba Attahiru Gunna na II, yana shekara daya ke nan kan karagar mulkin masarautar, bayan rasuwar tsohon sarki Malam Salihu Tanko, wanda bayan karbar takardar shaida daga gwamnatin jiha bisa jagorancin gwamna Abubakar Sani Bello, ya jiran karbar sandarsa a matsayin cikakken sarki mai sanda na daya a kowani lokaci daga yanzu.