Buhari Zai Tafi Sakkwato, Kwara, Ogun Da Jihohi 7  Don Kamfen Tinubu Da Kansa

Buhari Zai Tafi Sakkwato, Kwara, Ogun Da Jihohi 7  Don Kamfen Tinubu Da Kansa

Jam'iyyar APC ta ce shugaba Muhammadu Buhari a shirye ya ke ya halarci wasu tarukan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasarta da kansa nan gaba, Daily Trust ta rahoto. 
A cikin sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, Direktan watsa labarai kuma babban kakakin kwamitin kamfen din Tinubu/Shettima, Festus Keyamo, SAN, ne ya fadi hakan a jadawalin kamfen da aka fitar a baya-bayan nan, ya ce shugaban kasar zai halarci kamfe a jihohi a ƙalla goma. 
Keyamo, wanda shine karamin ministan ayyuka da kwadago, ya ce Buhari a shirye ya ke ya halarci kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC. 
"Idan za a iya tunawa, Shugaban ƙasa duk da ayyuka sosai da ya ke da shi, ya halarci ƙaddamar da kamfen ɗin ɗan takarar shugaban ƙasa a Jos ranar 15 ga watan Nuwamban 2022. Bayan ya amince ya zama ciyaman ɗin kwamitin kamfen ɗin shugaban ƙasa na jam'iyyar mai mulki.
"A jadawalin da aka fitar jiya (5 ga watan Janairun 2023) shugaban ƙasa zai halarci kamfen a ƙalla a jihohi goma. 
"Jihohin su ne Adamawa a ranar 9 ga watan Janairu; Yobe a ranar 10 ga watan Janairu; Sokoto a ranar 16 ga watan Janairu; Kwara a ranar 17 ga watan Janairu; Ogun a ranar 25 ga watan Janairu; Cross Rivers a ranr 30 ga watan Janairu; Nassarawa a ranar 4 ga watan Fabrairu; Katsina a ranar 6 ga watan Febrairu; Imo a ranar 14 ga watan Fabrairu da na ƙarshe Jihar Lagos State a ranar 18 ga watan Fabrairu." 
Sanarwar ta cigaba da cewa PCC na son miƙa godiyarta ga Shugaba Buhari shugaban jam'iyya bisa jagorancinsa na gari da lokacin da ya ware don tattara kan yan jam'iyya da magoya baya. 
An kuma yi kira ga yan jam'iyya da masoya su fito kwansu da kwarkwata kamar yadda suka saba don halartar ralli din don cimma nasara da izinin Allah.