Buhari Ya Yi Alkawalin Mika Mulki Ga Duk Jam'iyar Da Ta Samu nasara a 2023

Buhari Ya Yi Alkawalin Mika Mulki Ga Duk Jam'iyar Da Ta Samu nasara a 2023

 

Yayin da ya rage saura watanni 18 da cikar mulkinsa shekaru 8, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a ya tabbatar wa kasashen duniya shirin gwamnatinsa na mika ragamar mulki ga wadanda suka lashe zabe na gaskiya a Najeriya nan da shekarar 2023.

 

Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu ana fuskantar barazana ga mulkin dimokuradiyya a yankin yammacin Afirka ta hanyar kwace gwamnati ba bisa ka'ida ba daga sojoji.

 
Tun lokacin da muka hau kan karagar mulki a shekarar 2015, mun sami damar bullo da hanyoyin tabbatar da sahihin zabe da gaskiya.  Mun karfafa manyan hukumominmu na yaki da cin hanci da rashawa tare da hadin gwiwar abokan huldar kasa da kasa kuma mun dauki matakai da tsare-tsare da dama na yaki da cin hanci da rashawa.”
 
A cewarsa, Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro da ke barazana ga dimokuradiyya, don haka ya yi kira ga abokan huldar duniya da su ba da goyon baya ga kokarinmu na magance tashe-tashen hankula da ta'addanci.
 
DIMOKURADIYYA