Buhari ya sanya hannu ga ƙudirin dokar Man Fetur

Buhari ya sanya hannu ga ƙudirin dokar Man Fetur
Buhari ya sanya hannu ga ƙudirin dokar Man Fetur

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan sabuwar dokar ƙudurin Man Fetur na shekarar 2021 ta zamo doka. 
Yayin dayake aiwatar da aiki daga gidansa na tsawon kwanaki biyar, kamar yadda Kwamitin Shugaban kasa mai kula da Cutar Korona ta bukata, bayan dawowar Shugaban daga London a ranar Juma'a 13,ga watan Agusta, Shugaban ya amince da dokar ranar Litinin 16 ga watan Agusta, don cika nauyin da dokar ƙasa ta rataya masa. 

 A bayanin da  Femi Adesina  ya fitar ga manema labarai ya ce  za a aiwatar da bikin na Sabowar dokar a ranar Laraba, bayan ranakun da aka umarci Buhari ya killace kanshi. 
Ya ce dokar na kudurin Man fetur, zai samar da  kula da tsari ga kamfanin Mai na ƙasa, Cigaban yankunan da ake aikin Mai da Sauran harkoki. 
In ba a manta ba majalisar Dattawa ta amince da ƙudurin a ranar 15 ga watan Yuni, 2021, yayin da Majalisar waƙillai ta ƙasa itama ta amince da dokar ranar 16 ga watan Yuni, hakan ne ya kawo karshen tsawon lokaci da ƙudurin yayi yana dako.