Buhari Da Gwamnoni 19 Suka Goyi Bayan Cire Mai Mala  -- El-Rufa'i

Buhari Da Gwamnoni 19 Suka Goyi Bayan Cire Mai Mala  -- El-Rufa'i
 

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce sai dai Mai Mala Buni ya dawo a matsayin gwamnan Jihar Yobe, amma ba a matsayin shugaban riƙo na jam'iyar APC ba domin Shugaba Buhari da gwamnoni 19 a kalla suka goyi bayan a cire shi kan mukaminsa.

 
El-Rufai ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi a shirin 'Politics Today' a tashar Channels TV a jiya Laraba, ya ce bayan hawan gwamnan Neja Abubakar Sani Bello an samu cigaba a jam'iyar kan aikin da aka daura masa na gudanar da babban taro na kasa.
 
A cewar El-Rufa'i, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na da cikakken goyon baya ga Gwamnan Jihar Naija, Abubakar Sani Bello kan ya karbi ragamar riƙe jam'iyar.
 
Ya kuma zargi Buni da yin maƙarƙashiya don kada a yi babban taron APC na ƙasa a ranar 26 ga watan Maris kamar yadda a ka tsara.
 
El-Rufai ya ce Buhari ya faɗa musu cewa lallai Abubakar Sani Bello ya karɓe jam'iyar nan kuma ya Banu umarnin a yi duk abin da ya dace a tabbatar an yi babban taron APC a ranar 26 ga Maris.
 
Ya kuma yi zargin cewa har umarni Buni ya samo da ga kotu domin hana wannan taron na APC amma sai ya ɓoye maganar.