Bayyanar Hoton Tambuwal Da Musa Kamarawa Ya Haifar Da Cece-ku-ce A Sakkwato

Bayyanar Hoton Tambuwal Da Musa Kamarawa Ya Haifar Da Cece-ku-ce A Sakkwato

A yau Lahadi da safe aka tashi da hotunan Musa Kamarawa wani mai laifi da aka kama domin zarginsa da hulda da 'yan bindigar da suka addabi yankin Sakkwato ta gabas tare da Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, a wani gefen ya dauki hoton tare da mataimakin gwamna Manir Muhamad Dan'iya.

Bayyanar wadan nan hotuna ya sanya mutane a jiha musamman a kafar sada zumunta ta facebook suka yi ta fadin albarkacin bakinsu kan hotunan.

Ra'ayin mutane ya bambanta a gefe uku in da wasu ke ganin wadannan hotunan bana gaskiya ba ne hada su aka yi, wasu na ganin gaskiya ne amma alakar aiki ce ta neman bayanai ta sanya haka, wasu na ganin dai akwai lauje a nadi ganin hotunan sun bayyana ne bayan da bidiyon matashin ya fita in da 'yan sanda ke masa tambaya.
   

Bashir Altine Guyawa Isa shugaban rundunar adalci ta Kasa ya bayyanawa managarciya ra'ayin kan yadda yake kallon hoton, ya ce au nawa aka ga mai tabka laifi tare da masu iko ko kasa ko manyan 'yan siyasa, duk wanda kasan yana aikata laifi ana iya amfani da shi, Musa dai gwamnatin Sakkwato da Zamfara sun yi amfani da shi ya san manya a cikin gwamnati, yanzu haka ina da kwafin takardar da aka ba shi S.A  a Zamfara.

Guyawa Isa ya ce Wannan ba bakon al'amari ba ne mutane ire-irensu an sha amfani da su domin a cimma biyan bukata kuma da an samu abin da ake so a jefar da su "Musa ya kammala aikinsa ne tsakanin gwamnatin Sakkwato da Zamfara sun jefa shi in da suke so fakat, shi ne gaskiya al'amari."

Wannan kenan ba abin mamaki ba ne? ya ce "eh domin gaskiya ne hotunan nan ba karya ciki, ya yi lokacin da ake bashi kwangila yana kaiwa fulani dussa, abubuwan ba boyayyu ba ne kamar irin hoton da aka nuna ne na kwamishinan tsaro tare da dan bindiga Turji lokacin ana son a rungumo su ne domin samun bayanan da ake bukata don kwantar da hankalin jama'a amma sun ka finjire, an yi amfani da su domin samun biyan bukata ta masu iko da siyasa, a cewar Guyawa Isa.