Home Labarai Bayani kan yadda aka yi yinƙurin juyin Mulki a Nijar

Bayani kan yadda aka yi yinƙurin juyin Mulki a Nijar

34
0

An shiga ruɗani a Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar, bayan jiyo karar harbe-harbe da fashe-fashe a kusa da Fadar Shugaban Ƙasa da filin jirgin saman Diori Hamani a safiyar Asabar.

Rahotanni sun ce an kuma kai hari a wasu muhimman wuraren soji, lamarin da ya haifar da fargabar yiwuwar wani yunƙurin juyin mulki, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da cewa an samu juyin mulki ba.

Hukumomin ƙasar sun ce jami’an tsaro sun ɗauki matakan da suka dace, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankula.

Rahotannin farko sun nuna cewa an samu nasarar karɓe iko da wasu wurare, yayin da yanayin tsaro a wasu sassan babban birnin ke ci gaba da kasancewa cikin rashin tabbas.

Abin da ya ƙara jan hankali shi ne yadda wannan lamari ke faruwa ne a ƙasar da ke ƙarƙashin mulkin soji tun bayan juyin mulkin 2023, wanda ya kawo Janar Abdourahamane Tiani kan karagar mulki.

Ana ci gaba da bibiyar halin da ake ciki, musamman ko harbe-harben na da alaƙa da yunƙurin kifar da gwamnatin soji ko kuma wani harin tsaro ne na daban.

Ministan Tsaron Nijar, Janar Salifou Modi, bai yi ƙarin haske kan ko akwai waɗanda suka rasa rayukansu ko kuma waɗanda suka ji raunuka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here