Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmed Aliyu Sokoto yayi kira ga jama'ar jihar nan dasu ci ga gaba da zaman lafiya tare Kuma da kiyayewa da bin doka da oda.
Gwaman yayi wannan Kiran ne a wata sanarwa da Mai magana da yawun sa Abubakar Bawa ya fitar akan hari da aka Kai akan wani Usman Buda Mai Hanji da ake zargin yin kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. a babbar Mahauta(mayanka) ta Sakkwato da safiyar Lahadi.
Gwamnan ya yi kashedi ga jama'ar jihar nan akan yin duk wani yunkuri ko kalami da zai iya taba kima da darajar manzon Allah SAW, musamman ma dai a gari irin Sakkwato wanda gari ne na musulmai.
Ahmed Aliyu ya Kara da cewa mutanensa nada matukar soyayya da kauna ga Annabin Rahama ta yadda ba za su yi wasa da taba janibinsa ba, kan haka ya bukaci alumma dasu mutunta manzon Allah SAW.
"Ina kira ga alummar jihar nan da mu kaucewa daukar doka a hannu, a maimakon haka su kai rahoton duk wani laifi ko zargin batanci ga hukumomi don yin abinda ya dace"
"Addinin mu bai lamunta da mu dau doka a hannu ba don haka mu kasance masu bin koyarwar addinin" inji gwamnan.
Gwamnan ya Kuma Kara da cewa Gwamnatin sa ba zata taba daukar batun yin batanci ga fiyayyen halitta da sassauci ba, yana Mai cewa zata tabbata an hukunta duk Wanda aka kama da yin batanci ga fiyayyen halitta a bisa ga tanadin shara'ar musulunci.
Haka ma gwamnan ya bada tabbaci cewa a shirye gwamnatin sa take don ganin ta kare rayuka da dukiyoyin alummar ta.
Gwamnan ya Kuma ja kunnen masu nemen tada zaune tsaye dasu daina jihar Sakkwato ba wurin da za'a yiwa doka karan tsaye ba ne a kwashe lafiya.
Jami'an 'yansandan jihar Sakkwato sun tabbatar da mutuwar mutum daya Wanda ake zargi da yin bataci ga Annabi Rahama bayan fusatattun jama'a sun dirar masa aka yi masa rauni ya ko'ina ya rasa ransa a asibitin koyarwa ta Usman Danfodiyo.
Mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar ASP Ahmad Rufa'i a bayanin da ya fitar ya nemi mutane su cigaba da gudanar lamurransu bisa doka ba wani firgici za a Kuma binciki lamarin in har akwai wadanda suka yi laifi za a hukunta su.