Bayan dogon lokaci gwamnatin Sakkwato ta fara waiwayar 'yan gudun hijira 

Bayan dogon lokaci gwamnatin Sakkwato ta fara waiwayar 'yan gudun hijira 
Bayan daukar dogon lokaci in da gwamnatin ta shafe sama da shekara biyu saman mulki ta fara waiwayo 'yan gudun hijira da matsalar 'yan bindiga ta raba da muhallansu.
A jihar Sakkwato a Kowane yanki daga cikin yankuna uku a jihar suna tare da 'yan gudun hijira, a yankin gabascin Sakkwato wasu mutane da yawa maza da mata sun tafi jamhuriyar   Nijar   don neman mafaka a can, in da suka yada zango a jihar, Dosso, Maradi and Tahoua.
 
Gwamnatin Sakkwato da ke ci ba ta fitar da adadin yawan sansanin masu gudun hijira a jiha da wajenta ba, balle ma a san yawansu, abin da mutane ke gani sakaci ne na gwamnatin hakan ya sa ta shafe shekaru biyu ba tare da tura tawaga zuwa kasar Nijar don ganin halin da 'yan asalin Sakkwato dake can suke ciki ba.

'Yan gudun hijira suna cikin tasku da yakama gwamnatin jiha ta dauki matakin taimaka musu da abinci da wurin kwana, kyalle su a halin da suke ciki na kara yin barzana ga samun tsaron da ake kurarin ana son samar da shi a jihar.


A kokarin samar da sauki ga iyalan wadanda harin 'yan bindiga ya sama kwanan nan  a karamar hukumar Kware da Gwadabawa gwamnatin Sakkwato ta raba miliyan 69,750,000 da buhun shinkafa 210 ga wadanda lamarin ya shafa da iyalansu.
A wurin rabon tallafin a ranar Alhamis Gwamna Ahmad Aliyu ya bayyana hare-haren da ake kai abin takaici ne da suka sabawa lafiyayyen hankali, ya roki al'umma da su yarda lamari ne da Allah ya kawo, haka ma ya ba su tabbacin gwamnatinsa ta himmatu ga tsare jiha baki daya.
Gwamnan Ahmad ya nuna gwamnatinsa za ta cigaba da karfafawa jami'an tsaro a kokarinsu na kawar da masu tayar da kayar baya, ya kuma bayyana damuwa kan masu bayar da kwarmato infoma dake cikin al'umma, su ne ke kara kawo rashin tsaro.
"Ka ga infoma sun fi hadari fiye da 'yan bindiga, saboda ba yanda za a samu 'yan bindiga babu infoma," a cewar Gwamna.
"Shugabannin al'umma da addini suna da rawar da zai su taka wurin fadakar da mutane hadarin boye infoma a cikin jama'a kan haka akwai bukatar su tona asirin su."
Gwamna ya roki a hada kai a yaki matsalar tsaro, burin Gwamnatin sa ne ta kawo dawamammen tsaro a jiha baki daya.
Tallafin gwamna ya sanar da cewa iyalan wadan da aka kashe za a ba kowane iyali miliyan biyu da buhun shinkafa biyar, wadan da suka samu rauni za su amfanar da dubu 250 da buhun shinkafa uku.
A karamar hukumar Kware mutane 22 aka kashe a Gwadabawa mutane 11 ne wasu 11 suka samu rauni adadin kudin suka kama miliyan 69.75 da buhun shinkafa 210 aka bayar a ƙananan hukumomin.
Ana sanya rai wannan tallafin da Gwamna  ya soma bayarwa  ya mamaye dukkan kananan hukumomin jahar, tare da fito da wasu karin tallafi da zai kara saukaka wahalar 'yan gudun hijira.