Bashin Albashin Wata 10: Malaman Jami'ar Koyon Aikin Noma Ta Zuru Sun Koka

Bashin Albashin Wata 10: Malaman Jami'ar Koyon Aikin Noma Ta Zuru Sun Koka
Bashin Albashin Wata 10: Malaman Jami'ar Koyon Aikin Noma Ta Zuru Sun Koka
 
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
 
Malaman Jami'ar koyon aikin noma ta gwamnatin tarayya dake Zuru a jihar kebbi sun koka da rashin albashi na tsawon watanni 10.
 
Gwamnati ta manta da su a tsawon lokacin wanda hakan ya sa Malaman Makarantar shiga wani mawuyacin halin matsin  rayuwa.
Wani daga cikin malaman da ya buƙaci a sakaya sunan sa ya kira gwamnatin tarayya ta duba lamarin da suke ciki na rashin albashi har tsawon wata 10.
 
Majiyar ta ce "muna cikin mawuyacin hali bisa wannan lamarin ta yarda gwamnati ta yi watsi da mu kuma muna bukatar kulawar gwamnati a wannan lamarin".
 
A  nata ɓangaren itama wata malamar Jami'ar ta ce "za ta fara sana'a domin ana samun gibi yanzu a albashin Gwamnati  ta nemi bashi amma har yanzu ba ta samu ba,"
 
 
 
Malaman Makarantar, sun bayyana cewa rayuwa ta yi masu matukar wahala a wannan halin da suke ciki yanzu. 
Ƙokarin jin ta bakin hukumar Makarantar domin sanin halin da ake ciki domin samun cikakken bayani game da wannan lamarin abin ya ci tura, wayar jami'in hulɗa da jama'a na makarantar ba ta shiga a lokacin haɗa wannan rahoton.