Badala: Gwamnan Kebbi ya baiwa hukumar Hisbah da Zakka motoci shidda 

Badala: Gwamnan Kebbi ya baiwa hukumar Hisbah da Zakka motoci shidda 
Gwamnan Kebbi Dakta Nasir Idris ya ba da tallafin motoci shidda na aiki ga hukumar Hisbah da Zakka don saukaka aiki da samar da nasarar kawar da badala a jihar.
An  bayar da motocin a ranar Litinin a fadar gwamnatin jiha in da aka mika makullan ga shugabannin hukumomin guda biyu.
Gwamnan ya sanar da cewa bayar da  gudunmuwar na kunshe ne a cikin tsarin gwamnatinsa na bayar da kayan aiki ga hukumomi.
"Mun tabbata wadannan hukumomi ba za su iya gudanar da aiki ba kayan aiki ba, wannan gudunmuwar mun ba da ita ne domin cika alkawarin da  muka yi a farko na bayar da kayan aiki ga ma'aikatan gwamnati don su saukar da nauyin da ke saman kansu," a cewarsa.
Shugaban hukumar Zakkah Shaikh Umar Isah ya karbi makulli a madadin hukumar ya godewa gwamna kan lamarin.
Malam Umar Yahaya ya nemi gwamnatin ta dauki ma'aikata a hukumar Hisbah domin ya ki da badala da rashin gaskiya, ba ya yiwuwa sai da ma'aikata masu hazaka da son aikin.
"Kebbi na bukatar inganta hukumar Hisba a jihar bayan bayar da motocin aiki a kula da samar da ma'aikata da walwalar su, aikin hana ɓarna yana bukatar samun shiri mai inganci don samun tarbiya a cikin al'umma."
Kabiru Bunza ya ce gwamnati ta duba abubuwan da hukumomin Hisbah da Zakkah ke bukata sun wuce mota kawai don haka muna sa ran gwamnati ta  duba ta yi, ko zai rage aikin barna a cikin jama'a.