Badakalar Biliyan 37: EFCC Ta Gayyaci  Tsohuwar Minista Sadiya 

Badakalar Biliyan 37: EFCC Ta Gayyaci  Tsohuwar Minista Sadiya 

 

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati (EFCC), ta gayyaci tsohuwar ministar harkokin jin ƙai, Sadiya Umar-Farouq. 

Hukumar ta gayyaci Sadiya ne kan cigaba da gudanar da bincike kan wasu maƙudan kuɗaɗe N37,170,855,753.44 da ake zargin an karkatar da su a hannunta ta hannun wani ɗan kwangila, James Okwete.
An buƙaci tsohuwar ministar da ta gurfana a gaban masu bincike a hedikwatar EFCC, Jabbi, Abuja a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu, 2024, domin ta yi bayani kan badaƙalar zamba. 
Jaridar The Punch ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda ta musamman da ta gani a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba. 
Wani ɓangare na takardar na cewa: “Hukumar na binciken wani lamari ne da ya shafi karkatar da kuɗaɗe da ya shafi ma’aikatar kula da jin kai, bala’o’i da cigaban al’umma a lokacin da kike minista." 
"Dangane da abin da ke sama, ana buƙatar da ki kawo kanki domin tattaunawa wacce aka tsara kamar haka: Laraba, 3 ga watan Janairu, 2024. Lokaci: Ƙarfe 10:00 na safe." 
An kasa samun tsohuwar ministar domin jin ta bakinta a ranar Asabar, saboda wayarta ta nuna cewa a kashe take.