Babu wanda ya cancanta PDP ta tsaida takara Shugaban Kasa irin Tambuwal---- Bafarawa

Babu wanda ya cancanta PDP ta tsaida takara Shugaban Kasa irin Tambuwal---- Bafarawa

 

Daga Hussaini Ibrahim.

 

 Tsohon gwamnan Jihar Sokoto,Dalhatu Bafarawa ya bayyana cewa,babu wanda ya cancanta PDP ta tsaida takara Shugaban kasa a zaben 2023 ,irin gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

 

Dalhatu Bafarawa ya bayyana haka ne, a lokacin da ya ke gabatar da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ga 'yan Jamiyyar PDP a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

 
Bafarawa ya bayyana dalilin dan takara sa kamar haka,Hon Aminu Waziri ya goge a harkar siyasa yayi xan Majalisa wakilai Karo biyu ya kuma zamo Shugaban Majalisar a lokacinsa kuma yanzu haka , karo biyu ya a gwamnan Jihar Sokoto.wannan kadai ya Isa Jamiyyar PDP su aminta akan su tsaida shi takara Shugaban kasa.inji Bafarawa.
 
"Ya kuma kara da cewa, a zaben shekara ta 2018, Gwamna Tambuwal shine ya zamo na biyu a zaben fidda gwani na Jamiyyar PDP Atiku yazo na  uku.wannan ma abundibawa ga mu 'yan Jamiyyar PDP.inji Bafarawa.
 
Bafarawa ya kuma tabbatar da hajarsa bazatayi wuyar sayeba ga al'ummar kasar nan indai 'yan Jamiyyar PDP suka aminta da tsaida Tanbuwal takarar Shugaban Kasa.
 
A nasa jawabin Dan takara Shugaban Kasa Hon Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa,canjin cigaban al'umma suke nema shine ya sanya a shekara ta 2018 ,muka bar Jamiyyar APC dan Babu abunda ta tsinanawa al'ummar kasar illa sakasu cikin wahala da Masifa.gashin tsaro ya gagara al'umma na cikin mawuyacin hali dan idan kuka mara mana baya insha Allah wannan yazo karshe.inji Tanbuwal.
 
Kuma ya tabbatar ma al'ummar Jihar Zamfara cewa, shin dan gida ne yazo ya sanar da su cewa,yana neman taimakon su da addu'ar su da goyan bayan su akan wannan takara ta shi.
 
Mai masaukin baki , Mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Barista Mahadi Aliyu Gusau,ya tabbatar da cewa,zasu maramasa baya kamar yadda sukayi a wancan karon .kuma da yardar Allah nasara tana karemu insha Allah.
A