Babu batun ƙara wa'adin siyar da kujerun Hajji - Hukumar Alhazai ta Sakwkwato

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sakkwato tana sanar da cewa ba ta ƙara wa'adin sayar da kujerun aikin Hajjin bana ga maniyyata ba, musamman ma ganin cewa Hukumar Alhazai ta Ƙasa(NAHCON) ba ta ƙara wa'adin ba a hukumance.
A wata sanarwa Faruk Umar, Jami'in yada labarai da sadarwa na hukumar, sanarwar ta fito ne don kore rade-radin da ake yi a baya cewa an karin wa'adin.
"Maniyyata su lura da cewa ainihin wa'adin yana nan ba a ƙara, kuma su hanzarta su yi rajistar su akan ka'ida,"