Babban Buri:Fita Ta Ukku
Wurinda ta bar Hajiya Inna anan ta tarar da'ita, ko kallonta bata sake yi ba ta fice daga ɗakin a hasale, baki Hajiya Inna ta taɓe sannan ta ce "ai daɗa hwa anfara kenan."
MALLAKAR MARYAMAH IBRAHEEM.
SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU} MARUBUCIYAR MATAR ABDULLAH.
بسم الله الرحمن الرحيم
FITOWA TA UKU.
~~~Ƙara ware su na yi ganin lallai kuwa shi ɗin ne ya sanya jikina ɗaukan rawa , ƙafafuwana har neman kayar dani ƙasa suke yi.
Kallonsa na ke yi yayinda na kasa ɗaga ƙafa ta ko ɗaya sai faman haɗiyar yawu nake yi da matuƙar wahala.
Nunamin ƙofa yayi da farcensa yana me danna wayarsa da hannu ɗaya.
Sai lokacin na samu zarafin ɗagawa daga gunda nake na doshi hanyar barin ɗakin.
Samun nasarar barin ɗakin da na yi shi ne abu mafi sanyayamin rai, ina fitowa na saki wata irin ajiyar zuciya haɗi da dafe dai-dai gurin da nake sa ran nan zuciyar take.
A saman luntsuma-luntsuman kujerun Hajiya Inna na zube ina ƙara sauke ajiyar zuciya.
Shigowar Hajiya Inna ne ya fargar dani , na yi azamar miƙewa ina cewa da'ita ni zan wuce domin shirye-shiryen ɗaura girkin dare."
Kallona ta yi kan tace dani "kin haɗawa shalelena?" gyaɗa kaina na yi alamar eh, sannan ta ƙara cewa kema ki je ki ɗibo nima ki zubomin da irin 'yan kayannan na sama ina jin daɗi ne da su idan aka haɗa da ɗan wakennan."
Kitchin na dun fara na harhaɗo mata duk abinda ta buƙata sannan nima na haɗawa kaina kana na fice daga part ɗin.
Ina ficewa naci karo da 'yar Baba mukhtar wato Safiya dauke da ƙaton basket tasha uwar makeup sai karai-raya take yi.
Kallona ta yi a hankaɗe sannan taja tsaki ta wuce, bansan dalilin hakan ba.
Ba sallama ba komai ta hankaɗe ɗakin Hajiya Inna ta shige Parlourn tana faman ƙarewa ɗakin kallo.
Ɗago da kai Hajiya Inna ta yi tana aika mata da harara sannan tace da'ita "to taƙadiriya miye na shigomin ba sallama kuma sai kace wace ta shiga ɗakin uwarta?."
Ɗan shar mur ta yi sannan ta ce "na fa yi sallama Hajiya kece dai bakiji ba."
"Oh ni ce me kunne karkace ko? Wace ba ta jin abinda ake faɗa?".
"Ni dai ba wannan ba Hajiya Inna ina sweethart? nasan yana part ɗin nan?".
Ƙara sakar mata wata hararar ta yi kan ta ce "waye haka?".
"Allah kinsan wanda nake nufi Hajiya Inna plx ina yake?".
Taɓe baki Hajiya Inna ta yi sannan ta ce " a haka zaki ƙarƙare dai 'yar wahala, yana can" ta faɗa tana mai nuna mata hanyar ɗakin da yake.
Cike da yauƙi ta wuce ta gefen Hajiya Inna ta nufi ɗakin.
Ba sallama ta faɗa cikin ɗakin har lokacin yana nan zaune sai dai yanzu yana aikin cin ɗan wake ne yayinda laptop take a saman cinyarsa yana faman sarrafa ta.
Jin motsin shigowar mutum ɗakin ne ya sanya shi ɗago da dara daran idanuwansa ya zube su a samanta.
Tsaye take hannunta ɗaya riƙe da ƙugunta ɗayn kuwa riƙe da basket da waɗansu kuloli masu masifar kyau da ganinsu zaka tabbatar da sababbi ne, sai faman girgiza jiki take yi.
Ɗan taɓe lips ɗinsa ya yi sannan ya ɗauke kansa a kanta ya mayar zuwa ga aikin da yake yi.
Taku ta fara yi izuwa garesa sai faman girgiza jiki take yi, saman kujera ta zauna yayinda ta ajiye basket ɗin a ƙasa sannan tasa hannu ta fara fitowa da abubuwan dake ciki.
Haɗaɗɗiyar Sakwara ce da miya sai faman tashin ƙamshi take yi , sai lemon kwalba data fito dashi daga ciki.
Zuba masa a plate ɗin data zo dashi ta yi kana ta sa hannu ta janye plate ɗin ɗan waken da yake ci ta iza masa nata plate ɗin.
Ɗago lumsashin idanuwansa ya yi ya zuba mata hararar da sai da ta firgitar da'ita , ba tare daya ce uffan ba ya nuna mata ƙofar waje.
Zumbure baki ta yi sannan ta miƙe tsaye ta doshi hanyar waje, domin kuwa tasan ba abinda ya tsana irin mutum ya yi masa musu.
Cikin kakkausar murya da ban taɓa zaton yana da'ita ba ya ce "Dawo ki kaushe shirginki!."
Cak ta tsaya ba tare data ciyo ba , shi kuwa bebi takanta ba ya janyo ɗan wakensa ya ci gaba da ci.
Ganin tsayin baz ai kai ta ko ina ba ya sanya ta dawo jikinta a sanyaye ta fara harhaɗa kayanta.
Ko kallonta bai yi ba har ta kammala ta fice daga ɗakin.
Dogon tsaki yaja kana ya ce "zan gyara maki zama ne kwanannan".
Miƙewa ta yi bayan ya kwankwaɗi kunun ayarsa harda lashe baki sannan ya harhaɗa takardunsa ya shige ɗaki.
Gunda ta bar Hajiya Inna anan ta tarar da'ita, ko kallonta bata sake yi ba ta fice daga ɗakin a hasale, baki Hajiya Inna ta taɓe sannan ta ce "ai daɗa hwa anfara kenan."
Sai wuraren 6pm muka sauke abincin dare, sallama na yiwa ƴan uwana haɗi da nufar sashen Hajiya Inna domin nayi mata sallama.
Nunamin kula ta yii sannan ta ce "ki ɗauka ki kaiwa ƴan ƙannenki" kana ta ɗauko ₦500 ta miƙomin ta ce "ungo wannan ku saye sabulu."
Kular na ɗauko na kalleta inata faman zuba godiya ganin tana ci gaba da miƙomin kuɗin ne ya sa na girgiza kaina sannan nace "a'a Hajiya Inna ki barsu kawai , Nagode sosai da hidima damu".
"Ke amshi nace ba wani dogon jawabi na neme ki dashi ba" ta faɗa tana sakarmin harara.
Hannu biyu nasa na ƙarɓi kuɗin inamai ci gaba da zuba mata godiya, kana nayi mata sallama na fice daga part ɗin nata gaba ɗaya.
A gurin shaƙatawar gidan na taradda ƴan matan gidan waɗanda suke zazzaune a gurin a ƙalla za su kai su takwas , gaida su na yi su dukansu ba tare dana jira amsawarsu ba na ci gaba da tafiya ta.
Muryar ɗaya daga cikinsu ce naji tana cewa "iyayenmu suje su nemo abinci da zufan jikinsu amman azo a kwashe a kaiwa ƙattin banza waɗanda ba su san zafi nema ba su cinye."
Cak na tsaya ko banga fuskar wacce ta yi magana ba na shaida Muryar Safiya ce wacce bansan mina tare mata ba tun farkon zuwana gidan ta nuna bata muradina.
Ko waiwayota banyi ba na fice daga cikin gidan inamai tunanin maganganun ta dalla dalla harna isa gidanmu.
Tun a bakin ƙofar shiga gidan nake jiyo kukan ɗan ƙanena da azama na ƙurɗa kaina cikin gidan da sallama haɗi da tambayar "waye ya taɓa mana autanmu?."
Zazzaune na taradda su kama daga Mama har kan ƙannena mace da namiji wato A'isha da Umar sai kuma Autanmu dana taraddashi a kwance ƙasa yana faman kuka.
Kallon mama na yi da ajiye kular abincin dana zo da'ita ƙasa sannan na ce "miya faru Mama?".
"Wai yunwa ce yake ji, shi ne sanadin kukan nan kinsan yau bamu tashi da komai ba a gidannan banci nera ashirin dana saya masu koko tun safe shi da Umar, ni da A'isha kuwa dole azumin muka wuce dashi."
Wata ƙwallar tausayin kanmu ce ta samu damar silalowa daga kan kuncina, ba tare da nace komai na miƙe naje kitchin da kaina na ɗauko kwanukan da muke cin abinci a ciki na fito sannan na ɗaga Ahmad dake yashe a ƙasa naje na wanke masa fuskansa na dawo na buɗe kular da Hajiya Inna ta bani wacce ni kaina bansan miye a ciki ba, Abincin da muka dafawa baƙinmu ne ciki mai yawan gaske sai da kwaleliyar kaza dake cikin leda a saman shinkafar wacce taji kayan haɗi sosai.
Ɗibarwa Ahmad abincin nayi na miƙa masa , aikuwa sai ya fara ci hannu baka hannu ƙwarya idan ka ganshi dole ne ma ya baka tausayi.
Zubawa Umar na yi sannan shi ma na miƙa masa , na kalli A'isha nace "a kawo abincin ne ko zaki iyar da azumin ne sai dai tunkan na rufe bakina naji........
Za mu cigaba a gobe........
ƳAR MUTAN BUBARE CE!
MALLAKAR MARYAMAH IBRAHEEM.
SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU} MARUBUCIYAR MATAR ABDULLAH.
Maryamah