Ba’a rike adawa da rowa---Sakon Dan PDP Ga Sanata Tambuwal
Magoya bayan jam’iyar PDP suna kokawa ga irin wannan halin na jagoransu domin suna fadin siyasa musamman ta adawa ba ta iya tafiya da hakan abu ce da ke bukatar waiwaye da bayar da gudunmuwa gwargwadon hali.
![Ba’a rike adawa da rowa---Sakon Dan PDP Ga Sanata Tambuwal](https://managarciya.com/uploads/images/2023/04/image_750x_643bf3f1ef486.jpg)
Wani magoyi bayan jam’iyar PDP a jihar Sakkwato Abubakar Abdullahi ya wallafa sako ga tsohon gwamnan Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal a turakarsa ta kafofin sada zumunta in da yake cewa “don Allah a dawo gida a dubi mabiya jam’iyar PDP da idon rahama, tun bayan faduwa zabe babu ko na gode, ba a siyasa haka, shi ya sa muka ce a yi duk mai yiwuwa a ci zabe indan kotunan Nijeriya duk macuta ne, ba a rike adawa da rowa,” a cewarsa.
Wannan bayanin nasa ya jawo hankalin Managarciya ga irin kokawar da magoya bayan jam’iyar PDP ke yi ga jagoran nasu ganin yanda bai dauke su da muhimmanci da yakamata ba.
Sanata Tambuwal sama da wata shidda da ya sauka kan mulkin jihar Sakkwato ya fita batun magoya bayan jam’iyarsa gaba daya, a tsawon lokacin nan sau biyu kacal ya shigo garin Sakkwato shima wannan ba ganin magoya bayan ya zo ba, kusan ka ce wadan da suka yi siyasa saboda shi sun zama marayu a harkar siyasa domin ya yi masu jifan matattar Mussa(mage).
Magoya bayan jam’iyar PDP suna kokawa ga irin wannan halin na jagoransu domin suna fadin siyasa musamman ta adawa ba ta iya tafiya da hakan abu ce da ke bukatar waiwaye da bayar da gudunmuwa gwargwadon hali.
Wannan halin da Sanata Tambuwal ke yi matukar ya cigaba da shi a haka a shekarar 2024 ba shakka sai wasu mutane da bai yi zato ba sun karbe jam’iyar PDP hannunsa ya koma dan kallo a lokacin zai fara tunanin barin jam’iyar zuwa wata anan ne zai tabbatar da illar da ya yi wa kansa domin za a gina ramen da za a rufe siyasarsa gaba daya a jihar ta Sokoto.