Sakataren yaɗa labarai na yankin Kudu maso Kudu Mabel Oboh ya yi gargaɗi kan shigar fannin Shari’a kan abin da ya shafi harkokin jam’iya ta hanyar kotuna wannan yana kawo cikas ga dimukuraɗiyya.
Oboh ya yi magana kan hukucin kotun ɗaukaka ƙara na hana hukumar zaɓe ta aminta da zaɓen shugabanni na jiha da jam’iyar ta yi ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark.
Ya yi kalaman a Benin ya ce ana ta mahawara kan shigar fannin Shari’a ga harkokin jam’iyyar siyasa.





