Ba Abin Da Ya Samu Tambuwal A Tafiyarsa Sabon Birni---Gwamnatin Sokoto

Ba Abin Da Ya Samu Tambuwal A Tafiyarsa Sabon Birni---Gwamnatin Sokoto

 

Gwamnatin Jihar Sokoto  ta karyata maganar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal  ya ketare rijiya da baya a tafiyar da ya yi karamar hukumar Sabon Birni don yin ta'aziya ga iyalan wadanda'yan bindiga suka kone kurmus.

A wani bayani da mai baiwa gwamnan shawara  kan kafafen yaɗa labarai Muhammad Bello ya fitar ya ce duk da cewa gaskiya ne gwamnan da tawagarsa sun kai ziyara Sabon Birni ranar Juma'a amma "lafiya ƙalau" suka tafi suka dawo.

Wasu rahotanni da Daily Trust ta tattara sun ce 'yan fashin daji sun sake kai hari a yankin ne inda suka kashe mutum uku tare da jikkata wasu da dama kwana biyu bayan sun ƙona mutum 25 a cikin motar bas.
Bello ya ce "Labarin da ake yaɗawa na kokarin jikkata Tambuwal  ba gaskiya ba ne, wabda wata
kafar labarai ta “Critical Times.” ta wallafa," a cewar sanarwar.

Sanarwa ta nuna cewar mutane su jefar da wannan labarin domin karya ce maras tushe da makama.