Farfesa Aminu Abubakar babban jami’in zaɓen fitar da gwani na jihar Sakkwato ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya samu ƙuri’a 68,823, in da Rotimi Amaechi ya samu ƙuri’a 292, sai Hayatudeen Muhammad ya samu ƙuri’a 319.
Farfesa Aminu ya bayyana cewa an yanka rijista sama da dubu 69 a jihar Sakkwato, in da Atiku ya samu mafi rinjaye kan haka ya bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaɓen a jihar Sakkwato da gagarumin rinjaye.
Jami’in zaɓen ya faɗi sakamakon ne a gaban waƙillan hukumar zaɓe ta ƙasa da kuma jagororin jam’iyyar ADC a jihar.






