Home Rahoto Atiku ya buɗe shafi a yanar gizo da zai riƙa karɓa tambayoyin...

Atiku ya buɗe shafi a yanar gizo da zai riƙa karɓa tambayoyin ‘yan Nijeriya

5
0

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da wani shafin yanar gizo da zai bai wa ’yan Najeriya damar yi masa tambayoyi kan tarihinsa na siyasa, manufofinsa da kuma shirye-shiryensa na tafiyar da ƙasar.

Wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC, Phrank Sha’ibu, ya fitar ta bayyana cewa shafin mai suna “Ask AA” zai fara aiki da ƙarfe 8:30 na daren ranar Alhamis.

Sanarwar ta bayyana cewa shafin zai bai wa ’yan Najeriya damar aika tambayoyi kan muhimman batutuwa da suka haɗa da tattalin arziki, tsaro, fasaha, samar da ayyukan yi da kuma matakan da za a ɗauka domin rage tsadar rayuwa.

Haka kuma, sanarwar ta ce Atiku Abubakar da kansa zai riƙa amsa tambayoyin da aka aika ta wannan shafi, yayin da wasu daga cikin tawagarsa ta yaɗa labarai za su taimaka wajen bayar da amsoshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here