Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya yi kira ga ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International da ofisoshin jakadancin ƙasashen waje da ke Nijeriya da su shiga tsakani kan zargin kai hare-hare ga magoya bayan jam’iyyun adawa.
Hakan ya biyo bayan wani farmaki da aaki ka wani ɗan wasan barkwanci mai suna Osagie Daniel Idedia, wanda aka fi sani da Porkupyne, a birnin Benin na jihar Edo.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC , ya yi wannan kira ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, inda ya buƙaci masu ruwa da tsaki su ƙara sa ido kan yadda ake mu’amala da magoya bayan jam’iyyun adawa, tattara bayanai kan rikicin siyasa da kuma neman a ɗauki matakin da ya dace kan waɗanda aka samu da laifi, yayin da Nijeriya ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Tuni rundunar ƴan sandan jihar ta Benue ta fara gudanar da bincike kan lamarin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.






