Home Siyasa Atiku Ya Bukaci INEC Ta Bude Dukkan Fasahar AI Da Za Ta...

Atiku Ya Bukaci INEC Ta Bude Dukkan Fasahar AI Da Za Ta Yi Amfani Da Ita Domin Masana Su Tabbatar Babu Magudi

34
0


Atiku ya buƙaci hukumar zaɓe INEC ta buɗe dukkan tsarin fasahar AI da take shirin amfani da shi wajen tantance sakamakon zaɓen 2027 domin ya gayyato masana don su tabbatar ba’a shirya maguɗin zaɓe ba.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana tare da buɗe dukkan tsarin fasahar AI da take shirin amfani da shi wajen tantance sakamakon zaɓen 2027 domin masana masu zaman kansu su gudanar da bincike a kansa.
A cikin wasiƙar da ya aika wa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, Atiku ya nemi a bayyana yadda tsarin zai gano kura-kurai, dalilan da za su sa ya dakatar da sakamako da kuma matakan da za a bi wajen gyara duk wata matsala.
Ya kuma buƙaci masana tsaro ta yanar gizo, wakilan jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyin farar hula su samu damar duba lambar tsarin, bayanan da aka horar da shi da kuma bayanan ayyukansa kafin gwajin zaɓe na ƙasa baki ɗaya da aka shirya ranar 28 ga Nuwamba.
Atiku ya yi gargaɗin cewa bai kamata na’urar AI ta samu ikon gogewa, sauyawa ko toshe ingantaccen sakamakon zaɓe ba. Ya jaddada cewa Form EC8A da aka cike tare da sanya hannu a rumfar zaɓe shi ne muhimmin shaida, kuma bai kamata hukuncin na’ura ya maye gurbinsa ba.
Ya kuma nemi INEC ta samar da tsarin da jam’iyyun siyasa za su riƙa sa ido kan yadda ake tura sakamako kai tsaye, tare da bayyana hanyar da za a bi wajen ƙalubalantar duk sakamakon da AI ta yi wa alama.
Ɗan takarar ya kuma buƙaci Majalisar Tarayya ta gayyaci shugabannin INEC da sashen fasahar sadarwarta domin su yi wa ‘yan Najeriya bayani kan tsarin da matakan kariyarsa.
Atiku ya ce dole ne hukumar ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa babu wani ingantaccen ƙuri’a da zai ɓace ko a hana shi shiga sakamako saboda kuskuren na’ura.
–MIKIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here