Atiku Abubakar nada babbar dama ta iya lashe zaben 2023

Atiku Abubakar nada babbar dama ta iya lashe zaben 2023
Daga Aminu Amanawa, Sokoto.
Atiku Abubakar dai a yanzu dai wannan ce dama ta karshe da yake da ita na cikar burinsa na son mulkin Najeriya tun bayan zamowar sa mataimakin shugaban kasa a lokacin gwamnatin tsohon shugaban Najeriya Chief Olesegun Obasanjo.
Damar kuwa da Atikun keda a yanzu bai wuce irin burin samun shugaban da zai sauya a kalar Najeriya daga halin da take ciki zuwa wani dama daga ‘yan Najeriya keda buri musamman ma na matsalar Boko Haram a arewa maso gabas koda yake masana bangaren tsaron na cigaba da yabawa gwamnatin shugaba Buhari a wannan bangaren, sai kuma wacce ta kunno kai a arewa maso yamma ta garkuwa da mutane domin neman kudin fansa dama kai hari ga wadanda basuji basu gani ba, wanda a baya sai dai al’ummar yankin su rika karanta labaran hakan a wasu sassan Najeriya.
Baya ga wannan ma da akwai ta rikicin kabilanci da addini da a wasu lokuta ake samu a arewa ta tsakiya, sai kuma na masu fafutikar kafa kasar Inyamurai a kudu maso gabashin kasar nan, dama ta masu fasa bututun mai, duk wannan matsalace data shafi tsaro na kasa, wanda gwamnati mai ci yanzu ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta alkawarta magancewa, abinda har yanzu wasu ‘yan kasa ke ganin da sauran rina a kaba la’akari da yanda lamarin ke kara ta’azzara a wasu yankunan arewa dama kudancin Najeriya.
A bangaren samar da ayukka da bunkasa tattalin arziki ‘yan najeriya nan ma ba’a barsu a baya ba wajen cigaba da bayyana ra’ayoyin su, na halin matsin rayuwa  da suke ciki musamman na tashin farashin kaya na abinci, dama na amfanin yau da kullum.
Akwai kuman batun sufuri da samar da abubuwan more rayuwa irin su hanyoyi  da layin dogo wanda suna daga cikin abubuwan da jam’iyyar APC tayi galaba a zukatan ‘yan najeriya na tinanin share masu hawayen su a lokacin da jam’iyyar PDP ke shafe shekaru 16 bisa jagorancin ragamar Najeriya a lokacin.
Wannan ce ma ya sanya manazarta musamman masana kimiyyar siyasa ke ganin fa jam’iyyar PDP nada damar iya kafa shugaban kasa a zaben 2023 matukar suka tsayar da dan takarar da yake da nagarta, kwakwaro dama inganci.
Wace irin dama Atiku ke da?
Atiku Abubakar nada damar iya zamowa shugaban kasa a zaben 2023 fiye da sauran ‘yan takarar wasu jam’iyyu saboda wasu dalillai.
Na farko Atiku Abubakar ya kasance dan takarar da wasu ke ganin kwarewar sa ta haura ta babban abokin hamayyar sa da zasu fafata a zaben 2023 na jam’iyyar APC watau Bola Tinibu.
Atiku Abubakar baya ga kasancewar sa tsohon mataimakin shugaban kasa dake kwarewa a bangaren shugabanci dama sanin lungu da sakon Najeriya yafito a yankin da ya dade ba’a dama dashi ba wajen shugabancin najeriya, wannan masana na ganin zai bashi damar samun goyon baya daga al’ummar arewa maso gabas domin dansu ya zamo shugaban kasa a zaben 2023.
Dan kasuwa ne, Atiku nada kwarewa a bangarne bunkasa tattalin arziki, la’akari da jarin daya zuba a kasar nan wajen samar da kamfuna da suka dauki fiye da matasa dubu 200,000 ayukkan a kamfunan sa musamman kamfanin sarrafa ruwan sha na Faro, da jami’ar ta American University Yola da sauran  wuraren da yake da hannun jari, a wannan marra ake ganin matukar ya samu dama to fa zaiyi amfani da kwarewarsa wajen kafa masana’antun da zasu samar da ayukkan yi ga ‘yan kasa domin rage zaman kashe wando musamman ga wadanda suka kammala karatu ba ayukkan yi.
Atiku Abubakar nada wata damar da wasu ke ganin rashin tabuka komai na gwamnatin APC zai sanya ‘yan Najeriya kin sake bata wata damar a zabe mai zuwa  na 2023 domin sake jaraba PDP suga ko hankalin ta zai dawo domin sauya fasalin kasar.
Wani abu dake da muhimmanci ma anan shine samun wani hadin kai da PDP tayi a lokacin taron zaben fitar da dan takara, bayan janyewar da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yayi masa domin maslahar kansa dama ta jam’iyyar, wannan ma wani abune da ya bada mamaki matuka wanda ma ya janyo samun yabo gashi Tambuwal din daga Atiku wanda a baya yake ganin zai iya zamar masa barazana ga cikar burin sa.
Akwai kuma lamari na bangaranci wanda yake taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, wannan ma wasu na ganin zai taimakawa Atiku ta hanyar samun goyon baya daga Arewa yankin da yafito ya kuma fi yawan masu jefa kuri’a dama samar da kuri’u ga duk wanda yake son shugabantar Najeriya.
Aminu Alhussaini Amanawa, Dan jarida ne, kana dalibin nazarin kimiyyar siyasa ne a Najeriya.
07065654787