Argentina Project: Gwamnatin Sokoto ta binciki aikin Wamakko da Tambuwal

Argentina Project: Gwamnatin Sokoto ta binciki aikin Wamakko da Tambuwal

Kwamitin binciken gwamnatin Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Gwamna Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya kafa karkashin jagorancin Mai shari'a Mu'azu Pindiga a cigaba da binciken da yake yi ya gayyaci tsohon kwamishina a ma'aikatar kula da lafiyar dabbobi Alhaji Tukur Alkali don amsa wasu tambayoyi a shirin da Gwamnatin jiha ta kawo na samar da shanun Argentina sai kuma aka juya su da wasu shanu daban.
Shirin Gwamnatin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ta Kawo shi, a shekarar 2010 aka Sanya hannu a yarjejeniyar in da shirin zai lakume kudi sama da  biliyan biyu(2.6b), za a samar gonar ne a kauyen Tabani karamar hukumar Rabah.
A lokacin Wamakko ya fito da shirin ne na samar da shanun Madara da nama  domin ya fahimci jihar nada albarkatu da yawa matsalar yanda za a yi amfani da su ne jama'a su ci gajiyar.
Bayan da gwamnatin Sanata Tambuwal ta shigo a shekarar 2016 ya ba da sanarwar bayar da fili hekta 1000 don samar da in da za a yi aikin.
Tambuwal ya ce aikin za a yi shi ne a kananan hukumomi shida na jihar.
A shekarar 2018 Kwamishina Tukur Alkali a hirarsa da manema labarai ya ce gwamnati ta kashe sama da biliyan biyu(2.8b) ga aikin da ta gada wurin gwamnatin da ta gabata(ta Wamakko).
Mutanen Sakkwato sun zuba ido don jiran sakamakon binciken da kwamitin ya gano kan wannan aikin da ya lakume makudan kudi kuma bai tabbata ba.
Akwai bukatar sanin kwangilar an bayar da ita sau daya ne ko ta kai sau uku, da kuma abin da ya sanya aikin ya kwashe shekarru 13 ana maganarsa, da sauransu.