Arewa Ba Ta Iya Hana Kudancin Nijeriya Samun Tikitin Takarar Shugaban Kasa A PDP 2023----Wike

Arewa Ba Ta Iya Hana Kudancin Nijeriya Samun Tikitin Takarar Shugaban Kasa A PDP 2023----Wike

 

Hadin kan da jam'iyar PDP ta samu kafin babban taron jam'iyar kan wanda zai yiwa jam'iyar takara na neman ya mai da jam'iyar ta fada cikin wani sabon rikici.

Gwamnan Revers Nyesom Wike ya yi tsayin daka cewar dole dan takarar jam'iyarsu na shugaban kasa ya fito daga Kudancin Nijeriya.

Gwamnan ya yi kashedi kan kokarin danne dan kudu ya samu damar tsayawa hakan ba zai sabu ba yanda jam'iya ta aminta haka za a yi.
Ya ce suna ji kuma suna gani Kudancin kasa zai fitar da bayaninsa nan ba da jimawa ba, zance a ba su mataimaki ko wani daban bai taso ba.