APC ta lashe zaɓen kananan hukumomi a Kebbi

APC ta lashe zaɓen kananan hukumomi a Kebbi

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kebbi, KESIEC a yau Lahadi ta sanar da cewa jam'iyyar APC ta lashe zabukan kananan hukumomi da aka yi a jihar a ranar Asabar.

Aliyu Mera, wanda shi ne shugaban hukumar ga sanar da hakan a birnin Kebbi inda ya ce jam'iyyar ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 21 da Kansiloli 255.

Mera, ya ce jam'iyyu 17 ne suka shiga zaben ciki har da NNPP da LP da AAC da AP da SDP.

Ya sanar da cewa hukumar ta amince da sakamakon da jami'an zabe suka sanar a kananan hukumomin da mazabu.

Mera, ya kuma bayyana farin cikinsa kan yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Kamfain dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa PDP ta kauracewa shiga zaben, inda ta ce shugaban hukumar ta KESIEC mamba ne a jam'iyyar APC.

PDP tayi zargin cewa, shugabancin hukumar ba zai yi adalci ga jam'iyyun adawa ba.