APC Ga Tambuwal: PDP ba ta cikin Zukatan mutanen Sokoto
Kwamishinan yada labarai na jihar Sakkwato Alhaji Sambo Bello Danchadi a taron manema labarai da ya kira a satin da ya gabata ya sanar da tsohon gwamnan Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal halin da jam’iyar adawa ta PDP take ciki.
Kwamishinan ya ce muna shawartar Sanata Aminu Tambuwal ga abin da yake shi ne na gaskiya a yau jam'iyarsa ta PDP ba ta cikin zukatan mutanen jihar Sakkwato saboda yanda suka rike mutane za a dade ba su dawo hayacinsu ba kan gurbataccen shugabanci, "Gwamnatin Dakta Ahmad Aliyu ta kaddamar da aiyukka sabbi da tsare-tsare wanda za su shafe PDP gaba daya a jihar Sakkwato."
Ya ce Gwamna Ahmad Aliyu mutum ne mai fada da cikawa ba mai surutu ba, duba da yadda aka yi ciyarwar azumin Ramadan da yanda ake gudanar da manyan aiyukka a jiha.
Sambo Danchadi ya ce jam'iyar PDP tana cikin dimuwa da rashin makama tun bayan da ta sha kaye a babban zaben 2023, sai ta ke ta kame-kamen nuna tana nan raye, har suke magana wadda ba ta dace ba a lokacin watan Ramadan da ya gabata.
managarciya