Ana Zaman Zullumi Biyo Bayan Munmunan Hare-haren Yan' Ta'adda A Jihar Kebbi
Daga Abbakar Aleeyu Anache,
Al'amarin dai ya tilastawa mata da kananan yara, kimanin dubu 10: kaura cewa gidajen su a jihar kebbi don gujewa yan bindiga,
Rahotanni sun bayyana cewa al'ummar Danko Wasagu da ke jihar kebbi, a arewacin Najeriya sun tsorata biyo bayan wani sabon harin da yan bindiga suka kaiwa wasu kauyuka, a yankin,
Yan ta'adda sun kai wani hari a kauyukan a jihar kebbi, inda suka Kashe Mutane a kallan fiye da 100: kuma suka yi garkuwa da mata da kananan yara sakamakon hare-haren da suka kai kauyuka 10, a karamar hukumar Danko Wasagu, a jihar kebbi,
A cewar wani rahoton wasu mazauna kauyukan Chunoko da gidan kade da kuma wasu, yankunan Danko Wasagu, sun ce yan bindigar, sun mamaye al'ummarsu, sun kashe mazaje tare da lalata dukiyoyi,
Wani mazaunin garin yar kade ya bayyana cewa yan bindigar sun yi garkuwa da mata kuma sun shige wani kauye na kusa da garin mu, suka yi garkuwa da Mutane da dama,
Rahoton ya kara da cewa kauyuka da dama sun zama ba kowa yayin da mazauna kauyukan ke tashi da gudu zuwa acikin garin Ribah, da wasagu da Bena, da kuma garin Zuru,
Yanzu haka dai Mutane kimanin dubu 10, ne, musamman mata da yara suka tsere zuwa manyan garuruwa, da suke makwabta ka,
Tuni dai hukumomin tsaro a jihar kebbi suka dauki matakan dakile wannan Munmunan Hare-haren yan ta'adda.
managarciya