"Ana Jin Jiki:" Kusa a APC Ya Fadi Makomar Tinubu Idan Za a Sake Zabe a Najeriya

"Ana Jin Jiki:" Kusa a APC Ya Fadi Makomar Tinubu Idan Za a Sake Zabe a Najeriya

 
Kusa a APC, Barista Ismael Ahmed ya tabbatar da mawuyacin halin da ‘yan Najeriya se ke ciki a wannan gwamnati ta Bola Ahmed Tinubu. 
Barista Ahmed ya bayyana cewa zai yi wahala a iya fadi lokacin da ‘yan kasa za su fita da halin yunwa da babu da su ke fuskanta a halin yanzu. 
A wani bidiyo da Abdul-Aziz Na’ibi Abubakar ya wallafa a shafinsa na X, jigon APC ya kara da cewa babu yadda za a iya boye halin matsi da ‘yan kasar nan su ka fada
Ismael Ahmed ya fadi haka ne a wata hira da Seun Okinbaloye ya yi da shi a shirinsa. 
Barista Ismael Ahmed ya bayyana cewa zai yi matukar wahala shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a zabe idan har za a gwabza a yanzu. 
Ismael Ahmed ya ce; “Zai yi wahala, zai zama zabe mai wahala, tabbas. Zai zama zabe mai sarkakiya idan za a yi shi yau.” 
Daya daga cikin kusoshin jam’iyya mai mulki ta APC, Barista Ismael Ahmed ya ce akwai bukatar masana tattalin arziki a gwamnati su sanar da ‘yan kasa halin da ake ciki. 
Ya bayyana cewa su kadai ne za su iya fayyace lokacin da mutanen Najeriya za su fara sharbar romon tattalin arzikin da aka ce ana gyawara, saboda haka akwai bukatar su yi bayani.