ANA BARIN HALAL....:Fita Ta 45

ANA BARIN HALAL....:Fita Ta 45

ANA BARIN HALAL....

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe.

Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

Idan kana/kina sha’awar:

_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._

_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._

_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._

_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._

_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t

*Page  45*

*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559

*********
"Eesha ima so muyi zama na mutunta kai da amana, zan baki dukkan ƙaunata, kulawata, yarda ta, amanan kaina, kema haka naƙe so ki bani naki, duk wani abu dana miki bani so ki doshi kan kowa sai ni, idan kinga abin yafi ƙarfina kona kasa tsayawa akai ne zaki doshi iyayenki da shi, bana son 3rd party a tsakanin mu beauty, bana son tarukucen ftiends saboda gujewa matsalaloli, bana son aro da bayar da aro na sutura, bana son chin bashi, ina son ki girmama iyayena da ƴan'uwa na, ni kuma zan tare miki duk wasu fitina da zasu iya fitowa daga gefena,  Eesha ina son biyayyah da girmamawa, ina son kula sosai, kuma bana son ƙaryah akan komai" yana faɗa ya ƙura mun idon shi, sunkuyar da kaina ƙasa nayi ina maimaita abunda ya faɗa a ƙasan zuciyata ,  "ina sauraronki Eesha".
"Nidai bana son ka wulaƙanta ni ne kawai, ina so ka soni har tsufah na, kuma...kuma..",  sai nayi shiru ina murmushi,  shima murmushin yayi yana kallona,  "kuma bako son kishiyako"? Ya ƙarasa yana dariya sosai, nima dariya nayi ina juya kaina alaman a'a,   "nifa bawai kada ka ƙara aure bane bana so, idan Allah yasa bani kaɗai zaka zauna dani ba ae dole sai kayi, amma ni nafi so ka soni sosai kafin lokacin da zaka so wata",  na ƙarasa ina ɓoye fuskana a ƙirjin shi, dariya sosai yakeyi ya rungume ni gaba ɗaya ajikin shi, mun daɗe a haka jifa -jifa ina jin sautin murmushin shi mai kaman sautin dariya,  "Eesha na ina sonki sosai, ina roƙon Allah idan akwai rabon auren wata mata a tare dani kada Allah ya kaini wannan ranan, ina roƙon  Shi daya zama ke kaɗai ce rabona duniya da lahira,"  da sauri na ɗago kaina na dube shi,  "nifa bance kada kayi ba, idan ni kuma na mutu fah"?  Haɗa goshin shi yayi da nawa, hancin mu ma suka haɗu, "sai na zauna ni kaɗai, idan da yaran mu sai na basu kulawa sosai",  lumshe ido na nayi ina sauƙe numfashi a hankali,  "a'a zamu rayu tare insha Allahu",   na faɗa mishi muryah a hankali,,  shima shiru yayi bai sake cewa komai ba, sai chan wayan shi ta fara ringing, handsfree ya saka bayan ya ɗauka,  
"morning Babban yayah, nace ko za'a barka kafito muje muyi sallama da mutanen mu, sai muƙara sa mu gaida su mummy dasu goggo da bangajjiya ko? Har gidan su Ayshaa zamuje kafin baƙin namu sutafi ko"?
Ajiyan zuciya ya sauƙe bayan yaji dogon lissafin da M.G ya mishi,  "mutumin banza yau kuma nine ka yadda nadawo babban yayah ko? Tou ni dai ba'a bani izinin fita ba, amma kaɗan yi jira na ɗauki permission, duk abunda beauty tace shi za'ayi",  yana gama faɗa ya kashe wayan, sannan a hankali ya maida kanshi saman nawa ya kwantar, shiru banji yace zai fita ba, sai nine nayi ƙoƙarin cewa,  "yayah baka tashi ba"? Ƙara matseni yayi cikin jikin shi sosai yace,  "sai abun da kika ce ranki ya daɗe, ina jiran umirnin ki ne",   miƙewa nayi yana taimaka mun har na tsaya, murmushi na mishi ina gyara tsayuwana,  "amma zaka chanja kaya ko"? Kallon kayan yayi yana yamutsa fuska yace,  "dole na ae yadda kika ya mutsani nida kayan ae na chanja, don wannan ɗan sharrin idan ya ganni dasu zai kunce mun zani agaban yayah na",  ya faɗa yana wucewa ɗakin shi, nidai dariya yabani wai na ya mutsa shi,.

Cikin shiga mai kyau ya fito, hannuna ya riƙo mukayi hanyar waje, har jikin motan shi na raka shi, kafin ya shige yayi mun kiss a goshi yana buɗe motan ya shige,  "tsaraban me zan kawo miki beauty"?
  Ɗan lumshe ido nayi nace,  "kadawo mun da kanka gida lpy",  idon shi a ɗan lumshe yace,   "alƙawarin yau babu ihuu da faɗa ko? Kinga daga jin muryan ƙaton banzan nan ya zama cikakken ango ya barni"?,   juyawa nayi da gudu cikin gida, shi kuma murmushi yakeyi har ya bar gidan.


Ana idar da sallan la'assar su Aunty B suka zo dukkansu, fitan A.G kuma babu daɗewa wasu daga familyn maman shi suka zo tare da Hudah,  mun kai 1hr tare dasu suka mun sallama sukace saura su shiga gidan heedayah, cike da mutuntawa muka rabu, na haɗa musu tsaraban biki na basu,  don sunce mun gobe zasu koma, ƴan matan cikin ma basu kayan kwalliya da su panties, ina ganin Hudah sai farin ciki takeji sosai, don har fuskanta ya nuna hakan.
Kallo nah hafsy takeyi tana ta ƙunshe dariya, dana gajji na tambayeta meye takewa dariya, aiko sai ta kunce da dariyan gaba ɗaya, hadiza ce ta koreta tace ta tashi suje su gyara kitchen ita da ummitah, suna tura baki gaba suka wuce, hira sosai muka sha tare dasu Aunty B, sai wurin 5:00 suka tafi, har lokacin kuma  A.G bai shigo gidan ba, amma dai ban zauna ni kaɗai ba, idan waƴan nan sun tafi tou waƴan chan zasuzo, haka har akayi magrib sai ƙafa ya ɗauke, don ko abincin rana da aka kawo baƙi ne suka ci, hafsy sun mun wanke -wanken duk abunda aka ɓata, zuwan su kuma dama diffent jus Aunty b da Aunty j suka kawo mun,  aka shirga su a babban friedge ɗina, duk wanda suka zo akwai abunda za'a basu da kuma cake da cin-cin dasu diblan,  ganin bana sallah hafsy sai da takasa shiru tace,  "Adda yaushe kika gama period? Naga baki daɗe dayi ba kuma gashi yanzu ma kina yi"? Hararanta nayi nace,  "a'a wannan na ƙaryah nakeyi munafuka",  dariya duk suka fara, har sai da zasu tafine  Aunty B ta riƙo hannuna muka tsaya a ɗaki, "kada ki damu Ayshaa, sau da dama irin haka yana faruwa da amare, sai kiga lokacin period ɗinsu bai kai yadawo ba amma ya dawo, majority tsoro ne wasu kuma kayan gyaran mata da suka sha ne sai kiga period ya dawo, kada ki damu komai zai daidaita, kedai don Allah tsaftan nan dana sanki da shi ki dage, don yanzu zai dinga yawan shige miki ne, ki dage ko sau ɗaya kada yaji ƙarnin jinin nan, duk da nasan ke bada ga nan ba a kula da jiki amma plz ki ƙara beatyn besty",  rufe fuskana nayi ina murmushi, Aunty j na tsaye a gefen Aunty B itama tace,  "gaki dasu humrah da miski sisto plz kada kiyi wasa da ƙamshi a jikin ki, kuma kada kiƙi bashi haɗin kai ku kwana wuri guda duk yana ƙara shaƙuwa a tsakanin ku kinji"? Kai na ɗaga musu ban ƴadda na buɗe fuskana ba,  "idan akwai abunda ya rufe miki baki gane ba, gani ga jeeddah, ko wacce acikin mu babu shamaki ki ƙira mu wayar miki da kai kinji bestyn mu,  saboda dukkanmu gobe monday zamu koma",  Aunty B ta faɗa, buɗe ido na nayi ina kallon su kaman zanyi kuka,  "amma dai su yayah zasu zo mun kafin ku  tafi ko?"  dariya Aunty j tayi tace, "tare ma duk zamu zo idan za'a wuce airpot".
Har waje na rakasu suka tafi.

Bayan nayi wanka na saka wani rigan material ɗina wani pink riga da skirt, humrah na shafe jikina gaba ɗaya da shi, dayake duk kayana su fatima da Aunty B sun turara mun, sai yazama humrah nake shafawa kiji kaman yanzu akayi kabbasa, wasu oils masu daɗin gaske da Aunty ma'u ta kawo mun irin na saudin nan duk na shafe jikina dasu, hatta gashi na yasha nashi haɗin ɗan borno, ana idar da ishaa A.G ya shigo, daga ganin shi duk a gajjiye yake, ina biɗe mishi ƙofa ya buɗe mun dukka hannayen shi alaman nazo, nidai kasawa nayi na nuƙe kaina ina murmushi, ganin haka ya ƙaraso da kanshi ya rungumeni, duk da wunin da yayi da kayan amma ƙamshin shi mai sanyin daɗin nan ne ke tashi a jikin shi,  "baƙauyiyar amaryata mai gudun miji, yau kin sakani duk naji kunya a gaban abokane na, kowa ya gane bana fallin angwaye yadda M.G yake tayi, abu kaɗan zaka ganshi yana ta ɓallewa da dariya, har naji haushi nace ya tashi ya tafi, wani abokin mu ɗan Gombe ne yace yaga alaman A.G yana ruwa kenan, ko an kulle ƙofa an barni da sintirin parlor ko kuma baƙon mata ya hallara, sai da barrister ya dakatar dasu suka barni asha iska."

Sunne kaina nayi a ƙirjin shi bance komai ba, murmushi yayi ya ɗago fuskana yace mun zaije yayi wanka, har ɗakin sh yaja ni muka shiga domin yayi wankan, bakin gadon ya ajiyeni ya wuce toilet, nidai da ƙyar na daure nayi mintuna kusan uku zaune a ɗakin,  bana so yaga kaman ina gudun shi ne tun shigowan mu ban juya na fita ba, don wannan mummunan ciwon kanne naji ya sake sauƙo mun, bayan na zauna kuma sai nafara jin kaman numfashi yana mun ƙaranci a ɗakin, amma duk da haka na daure na zauna ina ta haɗa uban zufa, chan sai naga kaman inuwa ta gefena ya wulga, da sauri na juya inda naga wulgawan abun, amma banga  komai ba, chan naji kaman an wulga ta gab dani, ai babu shiri na miƙe nayi waje, ina fita kuma na sauƙe ajiyan zuciya, saboda sai naji wani ni'imah ya sauƙa mun lokaci ɗaya, wurin dinning naje na Ƙara gyara  filet ɗin abincin da aka kawo mana, ina zaune a parlon shiru ni kaɗai, chan sai gashi ya fito jikin shi da wasu kayan bacci blue masu kyaun gaske, suma shot wando ne da riga armless shigen irin wanda yasaka jiya, sai ƙamshin shi mai daɗi da yakeyi.

"yarinyar nan ya zanyi ma cire miki wannan kunya da tsorona ɗin nan da kikeyi ne kam? Wato baki son ganin fitowana haka ne yasa kika gudo nan ko"?
Murmushi nayi don jin bai gane abun da ya fito dani ba, bai ce komai ba ya miƙo mun hannun shi na kama ya miƙar da ni, dinning mukaje mukaci abinci, dayake gudun kurna ne aka kawo mana yasha naman kaji rugu-rugu a ciki,  "beauty wannan abincin yana ɗaya daga cikin favourite ɗina, sai ki kula da duk abincin da mummy zata na aikowa har tsawon 1week, don duk abunda nake so takeyi mum, tun daga breakfast, lunch, dinner".
Ɗaga kai nayi alaman naji, sannan muka ƙarasa, muna shan kunun aya, shima ƙura mun ido yayi yace, "ina son kunun aya sosai, yaji kwakwa da madara Eesha", murmushi na mishi ina ƙara maida hankali akan duk abunda yace yana so, a haka muka gama na tattare kayan nayi kitchen dasu don wankewa, shikuma inaga ya wuce ɗakine don ya wanko bakin shi, ina gama wankewa kuwa na wuce nawa side ɗin, nima baki naje na wanke sosai, daga nan na ɗauki wani cwemgum da Aunty ta bani mai ɗan karen ƙamshi nasaka a bakina, na ɗan ƙara shafa humrah kaɗan a jikina, ina zama a bakin gadona ban daɗe ba sai gashi ya shigo, kaina na ɗago na dube shi yana ƙarasowa kusa dani, wato Aunty nice ina son A.G a zuciyata, idan na kalli yadda idon shi suke a lumshen nan sai naji kaman na saka ihun daɗin mijina ya haɗu, ya haɗu mun irin yadda nake so miji ya kasance mun, amma ina wannan banzan tsoro da kunyan da nake ji sun hanani zuwa ga mijina, kyakkyawan mijina ma aji.

gefe na ya zauna, sannan ya saka hannun shi ya matso dani jikin shi, kaman wanda nake jiran hakan kuwa na lafe sosai a jikin shi na kulle idona,  "beauty kin gudo kin barni, a ɗakin nan kike so mu kwana ne"? Naji ya faɗa, nidai ban ce uffan ba ina lafe a jikin shi mai taushi da ƙamshi kaman bana namiji ba,  "ki chanja kaya ki saka na bacci tou beauty, wannan yanzu ae kin gajji da shi ko? Gashi A.Gn Eesha yana son ganinta da kayan bacci",   murmushi nayi, bayan na ɗan ja lokaci na daure nayi namijin ƙoƙari na tashi na wuce na buɗe walldrove na ɗauki kayan baccina masu ƙamshin daɗi, riga da wando armless pink colour, haɗawa nayi da wani hijab tsayin shi ya kai gwaiwa na, wucewa nayi zuwa toilet,  ina shiga wani zuciyar yace mun na sake yin wanka, haka na haɗa ruwa mai zafin gaske nayi wankan, pad na chanja bayan nashafa mishi misk ajikin shi, ina saka kayan na shafa misk ajikina da wasu oils dana riƙo su a hannuna, hijab ɗin na ɗaura akan kayan da suka amshi jikina, wando bai ƙarasa chan ƙasa ba sosai, rigan kuma armless ne, tsaraban daya kawo munne, tun lokacin naci alwashin saka kayan ranan farkona, saboda sun mun kyau a ido da kuma jikina sosai, fitowa nayi zuwa ɗakin da ƙyar, ina buɗe Ƙofan ya maido da kallon shi kaina, amma lokaci ɗaya ya ɗaure fuskan shi,  "kada ki ƙaraso mun da wannan abun a jikin ki, bana son haka beauty",  ya faɗa babu sassauci a fuskar shi da muryan shi,  babu yadda na iya haka na daure na cire, jikina har rawa yakeyi saboda kallon da naga ya bini da shi,  ƙafa yana sassarɗewa na wuce na maida hijab ɗin walldrove na ajiye, zan juyo kenan naji ya eungume ni ta baya, ajiyan zuciya yake saukewa da sauri da sauri, ni kuma ɗakin ne naji ya mun dummmm, ga lokaci ɗaya naji kaman na cika ɗakin tam, sai zuciyata da ta fara tafasa kaman ana hura mun wuta, bakin cikin daya ƙaru mun kuma jin sautin muryan A.G da ada yake mun daɗi, yanzu kuma naji shi babu daɗin sauraro yana ta jera ƙiran sunana kaman yaron da yake neman uwarshi ta shayar da shi,   "Beauty! Eeshaa!! Baby nah!! Plz ki barni ajikinki",  ai babu shiri naji zuciyata zata fashe, bansan ina da wani masifaffen ƙarfi ba sai da naji nayi jifa da A.G yayi taga-taga kaman zai kai ƙasa sai kuma ya dafa bango ya tsaya,  idon shi da suke masifan lumshen nan duk naga ya buɗe su lokaci ɗaya ya ƙura mun su,  "haba bawan Allah me kake nema dani ne kam? Ka kama hanya kabar ɗakin nan kafin na murɗe wuyanka kowa ma ya huta, wani irin fitinane haka"? Na furta ina jin kaman bakina zai yage da nake maganan tsabar girma da kaurin muryana, da sauri A.G ya runtse kunnen shi da hannun shi duka biyu, hattah idon shi a kulle suke yana tsaye wuri ɗaya, ni kuma gefe ɗaya sai hakki nake sauƙewa babu kakkautawa, kaina nayi saurin kawarwa lokacin danaga ya buɗe idon shi da duk sukayi ja yaƙura mun su,  "Eeshaa ta na miki laifine kam? Kina period babu abunda zamuyi kawai nazo jikinki ne na ɗan samu relief a zuciyana, plz Eeshaa nah plz",    ya haɗa dukƙa hannayen shi guri guda yana roƙo na,  hanyar waje na nuna mishi bada son raina ba,  "ka fita ko nayi jifa da kai",  jaka nasamu kaima da gaya mishi cike da tsawa,  amma baiji ba sai ya ƙara takowa kisa dani, aiko yana zuwa na zabga wani  uban ihu da ƙara na kai mishi duka da yaguni, da ƙyar ya iya haɗani wuri ɗaya ya matse ni, kokiwa muke tayi har ya samu ya kwantar dani akan gado, duk ya haɗa zufa lokaci ɗaya ga numfashin shi dayake ta sama da ƙasa, alaman abun shi yana kusa, ganin naƙi barin kukuwan yayi sauri ya ɗagani, hannu yasaka a aljihun shi ya ciro Inhela ya shaƙa, duk sai hakki yakeyi, ni kuma ina ta zabga kuka ina kwance, zama yayi gefe ɗaya ya kama kanshi yana ta sauƙe numfashi a hankali, zuwa wani lokaci abun ya ɗan lafa mashi kaɗan, ina ganin shi ya tashi yaje ya buɗe ɗakin ya fita, sai a lokacin naji normal kuka ya taho mun, duk sai naji tausayin A.G a zuciyata, ni kam mai yasa nake mishi hakane? Bawan Allah nan ko auren dole aka mun dashi bai chanchanci haka da ga wurina ba ko don darajan yayah Ahmad, ballantana Allah ne kawai yabar wa kanshi sanin irin so danakeyiwa A.G,  shiru zuwa wani lokaci naga bai dawo ba,  sai naji babu daɗi, tashi nayi nabi bayan shi, ko ma ciwon shi ne ya tashi ban sani ba?.

Parlor na nafito kawai sai na ganshi ya haɗa Uban tagumi yana zaune a parlon, ɗaguwa yayi ya kalle ni yadda na tsaya ina ta rera kuka, kallona yayi sannan yace,  "kije ki kwanta tunda haka kike so, zan barki har sai ranan da tsoron ya bar jikinki, don naga alaman an razanaki da maganan aurene kawai beauty",  kallon shi nakeyi ina share wasu hawayen da suka gangaro mun,  "tou ae naga kaman numfashinka yana wani iri,"
Murmushin dole yayi yace,  "yalafa kije ki kwanta".

Na daɗe tsaye a wurin ni ban tafi ba ni banje inda yake ba, shi kuma ko sake kallona bai sake ba, dana ga nafara jin bacci a tsaƴe sai na koma cikin ɗakin na kwanta, yiwa dai irin najiya ne, ina kwanciyar wani mummunan mafarkin na fara, wannan karon ihu nasaka a cikin baccin, in farkawa naga A.G riƙe dani yana tambaya na meye ya faru?.


*AUNTY NICE*