ANA BARIN HALAL..: Fita Ta Takwas

ANA BARIN HALAL..: Fita Ta Takwas

ANA BARIN HALAL..: 

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

*PAGE* 8

Yau ne habiba zata shigo amma shiru, sai ana fara ƙiran sallan magrib sai gashi ta shigo cike da farin ciki, hannun ta ɗauke da wani ƙaramin computer, ɗayan hannun ta kuma riƙe da wani leda mai ɗauke d turare masu shegen ƙamshi da kyau guda biyi, gefe nah tazo ta zauna jikin ta rawan murna ta ajiye ledan turaren ta buɗe computern ta mai shegen kyau ɗan ƙarami, "sisto kalli abunda Yayah Aliyu ya kawo mun, wallahi sisto yayi kyau nagode ki ƙara mun godiya a wurinshi, yace nagaishe ki ma sauri yakeyi," ta miƙa hannu ta ɗauko turaren ta buɗe tana cewa, "sisto ki ɗauki ɗaya a ciki, ranan ne muna hira nake bashi labarin turaren ashe ya saya mun, sai kawai naga ya haɗa mun da shi yau",  "wani irin ta miki godiya kuma? Ina ce dayazo ke kaɗai ya nema? Tunda hakane ae kin mishi godiya ya wadatar" cewar Aunty Bintu, wanda na lura ta fini jin zafin abun, nidai duban computer nayi nace, "gaskiya sisto yayi kyau kin chaɓa sosai, amma turare kuma ae wake ya sayo nima kuma kinsan ina da turare, sai next time idan ya kawo miki kya bani yanzu kam ae kya kai gida ki nunawa mamie ae", na faɗa ina miƙewa don zuwa yin alwala, shiru fatima tayi tana bin kowa da kallo, amma duk hankalinta kaman ba'a kwance ba, chan ta kasa jurewa ta dubi ƴar'uwarta tace, "Aunty nikan Aliyun nan saurayin waye a cikin su? Na ɗauka fa shine saurayin Ayshaa?"  da sauri habiba tace, "surayin ayshaa ne mana ni kawai shiri mukeyi sosai, kuma kinsan course ɗin mu iri ɗaya ne, shiyasa kullum hiran akan shawarwari yake bani inda zan dage da karatu, kuma laptop ɗina babba ne aka saya mun shiyasa yace zai saya mun wannan ƙaramin don zuwa school,"  "shima duk turaren na school ne ko"? Cewar fatima da ta bita da kallo ganin ta mayar da kowa shashsha, yare Aunty buntu ta koma yiwa fatima, daga nan kow a yayi shiru aka shige yin sallah, sai wurin ƙarfe takwas yayah mohd ya maida mu gida, nidai har zuwa lokacin bani jin sakewa a zuciyata, kuma abun mamaki har lokacin Aliyu bai ƙirani ba, kuma ina lura da su tun muna gidan yayah mohd ya ƙira habiba, babu daɗewa kuma mun dawo gida mun shirin kwanciya naga ya ƙirata, duk da bawani dogon magana sukayi ba, na dai ji tace mishi zata kwanta ne, sannan ta ƙara mishi godiya, tana aje wayan kuma tace mun sisto Aliyu yana sonki sosai, dubi abinda ya mun, duk fa saboda kece, nidai ko kallonta banyi ba ballantana nace wani abu, Data na kawai na buɗe na shiga whatsapp, jammy ce muka haɗu muke ta hiran cikinta da yadda ta ke tafama da laulayi, dayake a group ɗin mu ne, saiga maryam ma ta shigo a ka cigba da ita, muna ta yiwa jammy tsiyan ta kusa zama mamah, amsa ta dawo mun da shi akan nima ae ina hanya don taji wai za'a zo gaisuwa ae nan da ƙarshen next month, tunda mummy tace bata so abun ya wuce December dis year, saboda haka nayi shiru nima next year zan zama mamah, sai naji abun da takeji,
Lokacin kuma habiba ta hau, amsan da ta bayar ne yasa na ɗaga kai na kalle ta, kuma lokaci ɗaya naji gabana ya yanke ya faɗi, me habiba takeyi ne haka? Ki kama kanki habiba cewar jammy, domin ba yardar ki muke nema ba na ita jarumar muke nema, kuma mun samu, saboda haka go gefe besty, tafaɗa tan turo emoji ne gwaliyo wa habiba, ita kuma habiba ta sake maida mata da, wlh da gaske besty sai na amince tukun ayi december, idan ban amince ba babu abinda yaya Aliyu zai yadda ayi, idan baki yadda ba kuma ki tambayeshi, ita ma sai ta turo emojin gwaliyo, nan ma abunda ta sake faɗa sai da yasa na ɗaga kai na dubeta, duk da hankalin ta yana kan wayanta bani take kallo ba,
" tou ko dai kina tunanin tafiyan Ayshaa ta bar ki ke kaɗai ne? Sai ki fito da miji besty a haɗaku rana ɗaya, kowa sai taji da kewan ƴar'uwarta lokaci ɗaya" , cewar maryam, amma sai habiba tace "ai na fito da miji besty bayyanan lokaci kawai muke jira, amma soon", dariya jammy tayi tace, idan mu bamu da labari ae siston ki tana da labari, kuma gaskiya ya kamata ki gaya mana ae mun zama ɗaya, yanzu kam ma mun zama family ɗaya, tunda besty zata sake dawowa gidan mu",
Dariya habiba tayi, tace abun sirri ne, goodnyt sis jammy, ta faɗa tana sauƙa a online, ni kuma dama maryam ta dameni ta private akan bata ganewa abinda habiba ta faɗa ba, don Allah na maida hankali na dinga kula Aliyu muna hira, amma ita hankalinta baya kwance, na dai kwantar mata da hankali akan insha Allahu babu wani abu, zolaya ne kawai irin na habiba, a ƙasan zuciyata kuma hankali na ba a kwance yake ba, haka dai hiran namu ta watse.

Abubuwa na rayuwa sai tafiya suke kwanakin mu kuma yana ƙarewa, a haka har mukayi sati biyu babu wani ƙira daga Aliyu zuwa gareni, kuma bai sake zuwa gidan mu ba, amma kullum zasuyi waya babu adadi shi da habiba, wanda yanzu ba ta amsa wayanshi a gaba na, sai dai ta tafi side ɗinsu ta amsa, kuma yanzu sau dayawa zaman ta a side ɗin su yafi yawa, tare muke tafiya sch, amma idan ka ganmu tare irin na da tou sai dare, sau dayawa yanzu idan naji kaɗaici kawai sai na shiga wurin maryam.


Bayan wani ƴan kwanaki sai ummi ke tambaya na ko Aliyu yayi tafiya ne? Taga shiru ya daɗe bai zoba, amma sai nace mata yana nan kawai bai samun lokaci ne, a haka dai ummi ta mun ɗan nasiha akan rayuwa, wanda kullum duniya ita haka ne a tsakanin mu dukkan mu yaranta idan ta zauna sai ta mana nasiha, can sai hafsy tasa ka baki a maganan tana  ce mun Adda Ayshaa wai da gaske Yaya Aliyu ne ya saya wa Adda habiba laptop ɗin nan? haka raliya tagaya mun har tana wani maganan banzan ta chan, wai yanzu baku kula juna keda Yayah Aliyu",
Murmushi nayi bance komai ba, sai Ummi ce ta tsura mun ido cike da mamaki, " Ayshaa meye gaskiyan maganan da ƴar'uwar ki takeyi"? Inji ummi.

"ummi nima ban san yayah akayi ba, kawai naga ya kawo mata tsaraban shi da wasu turare, kuma ni baya ƙirana a waya, ita ya ke ƙira kullum, tou ummie ban san me yake faruwa ba", na faɗa jiki na a sanyaye.
 "Amma shine ayshaa baki taɓa ce mun komai ba? Hakan da kikayi dai dai ne?" ummie ta faɗa, shiru mukayi na wani ɗan lokaci, kaman kowa bazai sake cewa komai ba, chan sai ummie nah tace, "abinda nake so da ke Ayshaa yadda kikayi shiru baki cewa habiba komai ba tou haka nake so kada kicewa Aliyu komai, zato zunubi ne ko ganin baki kula shi, shiyasa hala suke zancen komai shida habiban, don ganin yadda kuke da ita Allah masani, nidai ta wurina kullum addu'a nake muku, kema ki dage da addu'a insha Allahu khairan" tsaki hafsy taja tana harara na taace, "ummi tou meye ma ita Adda Ayshaan bazata buɗe baki tayi hira da shi ba wai sai wata ce zata mata hiran? Allah ummie ce mun raliya tayi wai yace Adda habiba tafi Adda ayshaa kirki da son mutane, har tana wani cewa ae kirki gadon shi sukayi, tou me suke nufi da hakan"? 
Nidai hafsy bana son rikici da son faɗa, duk abinda tace kada taji bakin ki, bana so kice komai, nace Allah zai mana maganin komai, cewar ummie.


Ranan friday da dare dukkan mu mun hallara a babban parlon Abba, kasan cewar Abba yazo gari weeƙend, kowa yana nan banda yayah umar, da yake ƙarshen wata ne hattah yaya Ahmad ma yazo, kuma yayah mohd ma ya shigo, don a gidan shima yayi dinner da mu.

Gyaran murya Abba yayi, kowa ya maida hankalin shi kanshi, ni kuma lokaci ɗaya naji gaba na ya faɗi, don jiya a group jammy ke ce mana saturday za'a zo gaisuwa da tambaya, suna ta zolaya na, nidai banyi waya da Aliyu ba har yau, amma naji sunyi waya da mummyn shi, kuma Aunty Rakiya ma tazo gidan mu sunyi magana da ummin mu amma ni kuma bai ƙirani ba, amma a yanayin hiranmu a group sai naga kaman habiba tasan da hakan, duk sai naji ni a tsarge, ni ake nema amma ban san komai ba sai dai ƴar'uwata,  a haka na tsinto muryan Abba yana cewa, "Alhamdulillahi ranan laraba ƙanin mahaifin wannan yaron Aliyu ya ƙirani, akan ranan Asabar wato gobe insha Allahu zasu neman auren Ayshaa, saboda haka nayi waya da ƴan'uwa na gobe mutum biyu zasu zo, sai ni da Mohd da Ahmad zamu haɗu mu karɓe su, ke Ummien su munyi magana da ke tun ranan, akan Rakiya zata zo ku haɗu duk wani abu da za'ayi na karɓansu sai ku tsara, abun da ake nema sai ku gaya mun", sannan ya dawo da kallon shi kan habiba, "ƴan biyu na yakamata ki turo mun naki don na haɗa ku rana ɗaya na aurar da ku, domin burina kenan naga kunyi aure rana ɗaya da ƴar uwarki", ya faɗa yana riƙo hannun habiba, ita dai sai smilling takeyi tana sunne kai ƙasa, "Insha Allhu zaka aurar da su lokaci ɗaya Abban su, ita ma zata samo nata in......." mama bata ƙarasa addu'anta ba mamie ta chafke da "insha Allahu ma habiba ta samu don zama ta riga ayshaa ta fiya gidan auren, sai dai ita ta biyota daga baya", ta faɗa tana bin mamah da wani kallon banza.

Murmushi mai sauti Abba yayi yana duban mamie yace, " Ranki ya daɗe kin taɓa ganin inda mace ta tsara aure ba tare da mazaa ba, ae nine ko yayunsu masu yanke aure ba ke ba madam" ya faɗa yana maida kanshi kan habiba, cike da farin ciki ya sake tambayanta, "twins wai da gaske na samu surukin? Yh baki sanar da ni ba tuntuni sai yanzu naji?"  Abba shima gobe zai turo insha Allahu" habiba ta faɗa tana miƙewa da gudu tayi side ɗinsu.

Kallo mama ta bita da shi cike da mamaki, sannan ta dubi Abba tace, "Abban su wani irin maganane haka? Bamu taɓa ganin wani yazo ba sai dai muji wai za'ayi gaisuwan aure?, gaskiya ban taɓa jin irin haka ba"
"malama ae basai kin san neman ba, auren kawai yakamata ki sani, saboda ban san mugun nufin kowa ba kan yarah na, amma yanzu idan manya sun shiga kowa ma sai yaji", ta faɗa tana wani fari da ido kaman yarinya ƙarama, mudai lokacin Abba ya sallame mu muka bar shi da matan shi da kuma yayun mu.


Ganin hafsy zata takura mun da magana ni kuma gashi ji nake kaman kaina zai fashe da zuciyata, don ji nake Aliyu yama raina ni, raini mana  yana tunanin zaman auren habiba ne zata mun da bazai dinga magana da ni ba sai ita? Tou Alhamdulillahi itama habiban ta samu nata mijin naga kuma yayah zaiyi, ko yanzu zai na ƙirana ko bazai ƙira ba?  saboda haka sai na wuce side ɗin hajiya ummah kawai, itam ganinta zaune a parlon da mai aikinta suna kallon wani series na hausa ban wani zauna ba na wuce cikin ɗakin mu, domin nasan daga chan Abba nan zaizo da su yayah Ahmad, sai kawai na wuce ɗakin na kwanta, sannan na jawo wayana na shiga whatsapp, ganin maryam da jammy suna ta hira sai na musu sallama, ko amsawa jammy bata samu tayi ba ta ƙirani video call, harara na mata na wasa bayan na ɗaga, nasan gulmah ne kawai yake cinta, dariya ta kwashe da shi lokaci ɗaya, tana matar yayah meye ne yanzu duk kika zama wata silent da ke? Kin san fah ina masifar sonki shiyasa naji daɗi da yayah na ya zaƙuloki cikin ƙawaye na yace ga gwanar shi, abun ki sake mu tsara komai yadda ya kamata amma sai kike wani shareni kina basar dani, gashi kun koyi wani nuƙu-nuƙu keda ƴar'uwarki, wai har za'ayi tambayan auren ta gobe amma bata gaya mana mijin ba ballantana a ɗan gaisa a saba da juna, sai kawai yanzu take gaya mana, ni ban ma yadda da maganan besty ba, Allah dai ya kaimu goben, gashi abun yazo biyu idan d gasken ta keyi" ta faɗa tana wani dariyan rashin mutunci, nidai samun kaina nayi da sake jin faɗuwan gaba, ina kallon jammy cike da damuwa nace, " besty kodai Yaya Aliyu habiba yake son aure bani ba"? Ajiye bananan hannun ta da take ci tayi, da sauri tana duba na tace, "besty wani irin maganane wannan? Ta yayah ma haka zai faru? Yayah sokon inane?" murmushi nayi mai ciwo nace, "besty mu bar maganan wasa, nifa yafi 1month yaya Aliyu bai nemi waya na ba, zuwa wurina kuma ya daɗe, nifah ko wayan shi nagani shi da habiba ne, kuma yanzu ni ban taɓa ganinta da wani ba ko naji suna waya, idan ba shi ba, shi kaɗai yake ƙiranta kuma basu hira a gaba na, kinga ae hala ita ya koma yake so", na faɗa jiki a sanyaye, domin ni tun ranan da mukaje gidan Yayah mohd nake jin tsoro da fargaba, kuma tun ranan naji zuciyata ta  aminta da shi da auren shi, amma kuma tun daga ranan shi kuma ya ɗauke kanshi akaina.
"kan bala'i" naji amon muryan besty jammy, wanda har na manta ma akan waya nake, maida dubana nayi da hankalina kanta, "amma besty wannan shirmen magana ne, kuma haka nasan bazai taɓa faruwa ba don wallahi duk asirin uwarta mummy bazata bar ɗan ta ya faɗa ciki ba, gaskiya haka ma bazai yiwuba, kuma laifin ki nema besty, tun kwanaki maryam ta mun magana akai, na miki magana sai kika nuna ke ba haka ba ae ƴar'uwar kice, kuma hira take tayaki kawai, in banda ke yanzu besty ae duniyan fa ta ɓaci ba nagida ba bare duk cin amana ya kama zuciyar mutane, amma babu komai bari na neme mummy", da sauri na tare ta nace, "a'a besty don Allah kada ki nemi mummy, ae za'ace ina zargin ƴar'uwata kuma ita ma ae tace ta same miji gobe zai zo, saboda haka Allah ya kaimu goben, komai ma ae Allah zai bayyana shi, idan shine ma zata aura ae babu komai *ANA BARIN HALAL*.... ae don kunya, sai na bar mata nima Allah sai ya dube ni ya bani nawa rabon, tunda ita taga ya mata shima kuma yaga ta mishi, amma yanzu kam babu abinda zance don kada ya zama zargi.
"itace dai da shi za'a ce musu *ANA BARIN HALAL*.... dan kunya don ita ce ya kamata idan tana jin son shi ta haƙura don tsakanin ku da kunya, shima idan yaji ta mishi sai yayi haƙuri ya bari don kunya, kuma wallahi nasan ma insha Allahu haka bazai faru ba, don ae tare ya ganku kuma ya kware miki, ya ganta a lokacin mai yasa bai ce sai ita ba? Kayan dab da ƙasa kayan haushi" ta faɗa tana harara na, tana "nasan haushi na kike ji na aibanta ƴar'uwarki, wallahi besty ni halin mamamta ne bana so, don ita habiba mutum ne har da ƙari amma batayi dace da uwa ta gari ba, wani lokaci fah a ɓoye mamanta ta dinga zuwa gidan mu wurin mummy, da yake mummy ƴar no nonses ne ta watse ta bayan ta sallameta, inaa gaskiya bazai yiwu ba" ta faɗa tana mun sallama, nidai roƙonta nayi akan ta bar maganan Allah ya kaimu goben muga abun da Allah ya shiryah, harara na tayi ta kashe waya.

*AUNTY NICE*