ANA BARIN HALAL... : Fita Ta 43

ANA BARIN HALAL... : Fita Ta 43

ANA BARIN HALAL... : 

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe

Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

Idan kana/kina sha’awar:

_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._

_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._

_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._

_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._

_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t

*Page 43*

*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559


**********
Runtse ido A.G yayi a zuciyar shi ya furta. "*ALHAMDULILLAH*" 
ido suka haɗa da M.G, murmushi yayi mishi, shima M.G ya mayar mishi murmishin idon shi cike da ƙwallah, amma fuskar shi ɗauke da murmushi,  lumshe ido yayi ya cigaba da sauraran abun da akeyi, Daddy ne mutum na farko daya miƙa wa A.G hannu suka gaisa, yana congratulating ɗinshi, sannan suka haɗa hannu da M.G, sun kuyowa A.G yayi saitin kunnen M.G yace,  "yayah kaman kafin ɗokin wannan rana? Naga har hawayen farin ciki kake shirin zubarwa" M.G bai iya yace mishi komai ba har jama'a suka fara miƙa musu hannu ana taya su murna, daga nan suka wuce inda zasuyi recieption.
Alhamdulillah komai ya tafi musu yadda sukayi fata,  ana idar da sallan azahar suka shiga gida da abokansu suka gaida Mummy da ƙawayenta, ghotographer ya musu pics sosai, nan A.G ya haɗa rai wai M.G da tashi amaryar shi kuma tashi tana gidan su, haka dai suka gama daga nan suka ɗunguma sai gidan Goggo, nan ma sun haɗu da dangin M.G na fannin goggo da  na baban shi da suka shigo, nan ma anyi photona sosai, daga baya suka dingayi da yayunshi da iyalen su,  don hattah yayah auwal yazo ƙasan da matan shi da yaran shi, auren autan su mukhtarin goggo.

A gefen mu tun safe nasha wanka da ado da wata super ta mai kyaun gaske, an mun ɗauri mai kyaun gaske, gefe ɗaya kuma an kawo mun sabeer ɗina mun sha gayu sai photona mukeyi,  dawowan su yayah daga ɗaurin aure suka mun chaa da tsokana har sai da nayi kuka, yayah muhammad ne ya rarrashe ni ya saka naje na ƙara chanja kaya, shaddah na saka gedzner mai kyau, tasha adon ɗinki sosai, photona mukai tayi wuri dayawa ina rungume da sabeer, duk rauni ya cika mun zuciyata, haka akai ta hoto har da su Abba da familyn shi da suka zo, daga baya Abba ya ƙora kowa na gidan akayi family picture a parlon shi, hannu na ɗauke da sabeer ɗina.

Ana idar da sallan la'asaar akace a fito kai amaryah, don dama an shiryah don Abba yace ana idar da sallah za'a tafi, suna da buɗan kai da hawa.

Atamfah ta holland mai ktau nasaka, sannan aka nannaɗeni da lafayan da Aunty B ta kawo mun wani fari mai ratsin Red ajiki, atamfah ta kuma red ce.
Goggo da Aunty rakiya sai Adda ne suka kaini ɗakin ummie, inda take tare da ƴan'uwanta da ƙawayen ta, har ƙasa na durƙusa a gabanta, Bayan an buɗe taron da addu'a Aunty Rakiya tace,  "tou matar yayah ga ɗiyata na kawo miki kuyi sallama ki saka mata albarka, ki yafe ta kimata fatan shiga gidanta lafiya",  murmushi ummie tayi ta dube ni, a hankali muryanta na rawa tace,  "tou ni me Ayshaa ta mun a rayuwan danayi da ita? Albarka na kuma kullum ae yana tare da su",  kaina na mayar kan cinyarta na kwantar ina sheshsheƙan kuka, abun mamaki kawai sai aka ga ummie na kuka,   "haba Addah ke da zaki rarrashe ta kuma sai ki ɓuge da kuka"? Goggo ta faɗa tana ɗago ni tsaye akan mutafi, hannun ummie na riƙe, ina jin ta itama ta riƙe ni gam-gam,  haka dai aka lallaɓa mu muka fice.

Side ɗin hajiya ummah mukaje itama kukan dai tayi tayi tana saka mun albarka, daga nan sai wurin mamah, itama ban kwana na mata tayi ta jero mun addu'a da saka albarka, daga nan aka wuce dani ɗakin mamie, achan najiyo sautin kukan sabeer, sai naji duk zuciyata babu daɗi, haka na daure na tsuguna a gabanta, itama yadda akayiwa su ummie haka aka gaya mata, hannunta ta saka ta riƙo duka hannaye na ta riƙe su gam acikin hannayenta, addu'a take mun da fatan alkhairi, amma gaba ɗaya jina nake kaman na zabga ihu, saboda wani irin matse mun hannaye da tayi da ƙarfin gaske, wanda har sai da naji hannayen mu suna fitar da zufa nida ita, saboda babu space ɗin da iska zai shiga, adda'a tayi ta ja, daga baya kuma ta miƙar dani ta rungume tana muyafi juna, hannu Aunty Adda ta saka ta ɗago ni a jikinta muka fita,  hannu na kai sai tin hanci na nashaƙi wani warin da naji yana mun kaman na jan miski, ni tun asalina bana son warin shi, sai naji kaman miski kaman kuma wani ƙarni-ƙarni yake mun, muna shiga parlon Abba na goge hannun a jikin cottons ɗiɓ parlon da dabara, amma dai har jikin lafayyah na ina jin yana warin abun.
Muna shiga naje na durƙusa a gaban Abba, kuka nakeyi sukuma sunata mun addu'a da nasiha, a ƙarshe Abba yace muwuce kada mu ɓata musu lokaci, kafaɗu na ya riƙo na miƙe tsaye, hannun shi ya saka ya riƙoni muka wuce har waje, motan da aka kawo na ɗaukan amarya  Abba ya umurci su goggo da wasu a family su shiga, motan shi ya saka yayah muhammad ya matso mishi kusa da mu, baya ya buɗe ya saka ni, sannan shima ya shiga, ya umurci Aunty Rakiya ta shige gaban nashi motan.

Duk ƴan kai amarya ya saka suka wuce, muka bi su abaya, ashe kafin mu isa yasaka yayah Ahmad ya taho tare da A.G, masu rakiya dukka side ɗina suka wuce, mu kuma muna isa A.G suka fito a parlon shi suka tarye mu shida yayah Ahmad.

Muna shiga A.G ya rusuna yana nunawa Abba wurin zama, kujeran da Abba ya zauna ya manna ni a gefen shi na zauna, shi kuma yana rungume dani a kafaɗan shi, daga nan duk su Aunty dasu yayah suka nemi wuri suka zauna, shiru parlon ya ɗauka bayan an gama gaisuwa, ƙurawa A.G ido Abba yayi har zuwa wani lokaci mai tsawo, har sai da A.G yayi kaman ya koma ƙasa ya zauna, saboda ƙasa zai zauna Abba ya hanashi ya saka shi dole ya zauna kusa da Yayah Ahmad, duk sai A.G yaji kallon ya na tayar mishi hankali, har sai da Abba ya gama kallon shi na wani lokaci mai tsawo tukun yayi gƴaran murya yace,

"Aminu"!
Ɗago da kai A.G yayi a nutse ya amsawa Abba da  "na'am ranka ya daɗe"! 
Ya maida kanshi ƙasa yana ƙara risinawa, ido Abba ya maida kan Yayah Ahmad yace  "buɗe mana wurin da addu'a",   addu'a sosai yayi daya gama,  Abbah yayi gyaran murya yace
"A.G ga Ayshaa ƴata da ka nemi aurenta akan ka ganta ta maka kana sonta, ka zaɓeta akan ta zame maka uwar ƴaƴanka abokiyar rayuwarka right"? A.G ya ɗaga kai ya amsa da ehh,  "a'a ka buɗe bakinka ka amsa mun" Abba yace mishi,  "hakane Ranka ya daɗe, Allah ya ƙara girma,"  A.G ya faɗa.
"good, nakawo maka Ayshaa da hannu na ba saƙo ba, na kawota na danƙa amananta a hannun ka Aminu, na kawo ta na baka amanan ƴata mafi soyuwa a zuciyata, ƴata da idan an taɓa tou tabbas an taɓa zuciya da rayuwar usman" Abba ya faɗa yana nuna kanshi da hannun shi, hakan yasaka dukkan su suka sunkuyar da kansu ƙasa suna jijjiga mishi kai.
"Ayshaa amana ce a wurinka Aminu, haka kaima amana ne a wurinta, kuma na jaddada mata ban yadda ba ban ƴafe ba idan tayi wasa da amananka da yake kanta, ban yadda ba ta ƙunsa ma baƙin ciki, ban yadda ta ɓata maka ba sai a bisa kuskure, haka kaima,
Nakawo maka Aysha ne da sharaɗin ban baka aurenta don ka wulaƙanta mun ita ba yadda dayawa maza sukeyiwa matayen su a yanzu, ban yadda ka dakar mun ƴa ba, ban yadda ka kashe mun ita da baƙin ciki ba, idan Ayshaa tayi kuskure ka hukunta ta yadda addini ya tsara, amma dis time around duk wanda na bashi auren ƴata ya tozarta tou wallahi zanyi mishi hukunci daidai da abinda yayi, idan mutum yaji ƴata ya gajji da ita, tun wuri ya ɗauko ta a mutunce yadda nakawo mishi ita ya kawo mun abata,babu duka babu zagi".
Sannan ya tausasa muryan shi ya cigaba,  "Aysha ta samu tarbiyan da nayi imani da Allah ko bayan ranmu bazata bamu kunya ba, haka kaima nake kyautata maka kyakkyawan zaton na bawa ƴata miji nagari ɗan manyan mutane, na roƙe ku ka haɗa kanku ku zauna lafiya,  daga nan Abba ya dinga haɗamu yana mana nasiha mai ratsa zuciya daga ƙarshe Aunty ma tayi mana, inda take gayawa A.G, bawai Abba bai yadda da tarbiyan shi bane ya kawo ni har yaja mishi kunne,  a'a yayi hakane saboda karin magana da hausawa suke cewa, *IDAN MACIJI YA SAREKA.......* idan kaga tsumma dole ka kiyaye, saran da Aliyu yayi mishi ne yake firgice da shi, nan A.G ya nuna shi hakan ma yayi mishi, kuma ya ƙara jin aranshi Diamond mai tsananin daraja da tsada ya ɗauko, kuma yayi alƙawari da ƙarfin shi da lafiyar shi da komai nashi zai kare Ayshaa, insha Allah sai kowa yace gara da akayi.

Tashi Abba yayi tsaye ya ɗagoni muka tsaya, nidai ban da kuka babu abinda nakeyi, domin nasan Allah ya mun komai na rayuwa, ya bani gata na iyaye nagari, ƴan'uwa nagari , dangi nagari, kuma duk maso ƙaunata, gashi yanzu ya bani miji Nagari, mijin marainiya mai ƙaunata, Abunda zan nema kawai Allah ya zaunar dani da shi lafiya ya bamu zuriya ta gari, hannu Abba ya miƙawa A.G, da sauri ya ƙaraso gaban Abba amma yakasa bada hannun shi, har sai da Abba ya rungumu shi, hannuna ya cire a nashi ya ɗaura akan na A.G, ae kuwa da hanzari ya riƙeni sosai,  "Aunty nice nidai aduniya ban taɓa jin wani halittah na ɗa namiji daya taɓa riƙe hannu na bayan Abba dasu yayye na, gashi dai ɗabi'ace ta yayuna su rungumo mu, especially ma ni, Abba ma idan munje gaishe shi sau dayawa hannun shi yake miƙowa mu gaisa, amma ko yayah ishaq bamu taɓa riƙe hannun shi ba saboda kiyaye wa,  amma nidai ban taɓa jin hannu mai laushi ba irin na A.G, har tsoro naji a zuciyata nace, hala taurin nawa hannun zaiji, saboda laushim da hannun shi yake da shi banyi tsammanin akwai maza irin haka ba a duniya", Nidai murmushi nayi ina bin hajiya Aysha da ido, matse hannuna yayi cikin nashi, ina jin yadda hannun shin yake rawa, a haka Abba ya sake jaddada mishi amanan da ya bashi, sannan ya umurce shi daya sada ni da ɗakin shi, ina jin Abba yana zame hannun shi ajikina na zabura zan chafko shi, amma sai naji A.G yasaka dukka hannayen shi ya riƙe ni, ae kuwa da sauri na ƙara fashewa da kuka murya a sama nace,   "Abba na kada ka tafi ka barni,"  amma sai abba ya dafa kaina ya ƙara saka mana albarka yayi hanya fiya daga parlon, aeko da ƙarfi na ɗaga murya nace,  "Abba sisto ka zaka bari da wani"? Tsayawa Abba yayi chak a bakin kofan, ganin haka Aunty Rakiya ta ƙarasa ita da yayah Ahmad suka riƙe shi suka fice a parlon batare da ya juyo kaina ba, maida kallona nayi kan yayah muhammad da zaibi bayan su nace,  "besty kada ku tafi ku barni tsoro nakeji",  shima ɗan murmusawa yayi kaɗan bai kai chan ciki ba ya juya yayi waje batare da yace uffan ba, da sauri na maida kaina kan A.G, bakina har wani ɗan ɓari yakeyi nace,  A.G nikan kabar ni na biso, tsoro nakeji",
Hmmm A.G duniya ne, kawai Jawo ni yayi ya buɗe ƙofan ɗakin shi ya shige dani, muna shiga kuwa ya rungumeni tsaf a jikinshi bai bani amsa ba tanbayan da nake ta mishi na ina zai kaini ne? Kuka na fashe  dashi kawai mai ƙarfi, idan banyi ƙarya ba yakai sama da mintuna Goma muna a haka, har sai da aka ƙwanƙwasa ƙofan tukun naji muryan shi ƙasa -ƙasa yana tambayan waye?   "Hudah ce yayah",  ajiyan zuciya ya sauƙe, bai kuma ɓalle jikin shi da nawa ba yace,  "meye ne kuma Hudah"? 
"Mummy tace amaryar ka kaita za'a shiryata saboda buɗan kai, su Yayah M.G duk sun shiryah", tou kawai ya amsa mata da shi ta juya ta fice.
Ina jin shi yayi tsaki yace  "duk fitar M.G ne wallahi da wasu bidi'a, an ɗaura aure an kawo amaryah kuma meya saura ne nikan? Basai a haƙura da bidi'an da baida wani dalili ba? Hala Ƴan rakiyan kawo amaryan ma Abba ya kafa su sun tafi".

Nidai da sauri nace,  "wallahi suna nan, ina jin muryan su ma"  shiru yayi baice uffan ba,  kuma bai sake ni  na tafi ba.
A tsorace na sake cewa,  "mummy tace mu shiryah da wuri fa",   still dai bai kulani ba, shidai ya manna kanshi shi a saman kafaɗa ne, chan naji shi kaman mai barci yace,
"ko na ƙira Abba ne nagaya mishi suna nan basu tafi ba, don nasan yanzu zai umurcesu su tafi, mummy kuma babu matsalah Daddy ya isheta ta ƙyale mu da maganan bidi'an nan".
da sauri na har da fashewa da wani sabon kukan nace,  "wallahi nayi burin bikina ya zama akwai buɗan kai da hawa, udan ba'ayi ba za'a mun dariya, kuma bazan taɓa daina damuwan rashin yin ba",  aiko ina faɗin haka da sauri ya juyo dani ina kallon shi, dukkan hannun shi zube akafaɗa na, tsoro naji yadda naga udon shi a lumshe kaman bazai iya ganina ba, a raunane ya buɗe baki yace,  "zan shirya muje, zanyi abun da kike so, ai naji ance ba haramun bane ma, amma don Allah ana gamawa su tafi kinji beauty",  da sauri nake ɗaga mishi kaina alaman naji, nan kuwa ni kaɗai nasan wani irin masifaffen tsoron da nake ji a ƙasan zuciyata,  har ƙofan da zai fitar da ni daga sashen Shi ya rakani, yana riƙe da dukkan hannaye na ya ƙira Hudah, tana zuwa yace ta wuce dani side ɗina na shiryah, da sauri kuwa ta amsa mishi, dukka hannayenta ta saka ta riƙoni muka fice,  a parlor na muka samu su Aunty Rakiya da sauran ƴan'uwa,  nan ta riƙe ni muka wuce ɗakina, inda aka fara mun shirin fita wurin buɗan kai da za'ayi a haraban gidan su A.G.

*AUNTY NICE*