ANA BARIN HALAL....: Fita Ta 18
ANA BARIN HALAL....:
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 18
Ajiyan zuciya nayi, sannan na maida kaina na kwanta.
Washe gari tunda asuba Aunty B ta tashe mu, haɗuwa mukayi dukkan mu a kitchen muna haɗa breakfast na amaryah da friends ɗinta, ga kuma na yayah Ahmad da friends ɗinshi, don duk yau zasu koma, so kafin 8:00 mun gama komai, na amare aka kai side ɗinsu, na angwaye kuma yayah ne da yusuf suka zo suka ɗauka, nidai lokacin da suka zo ma na shiga wanka, 10:30 mun gama komai mun shiryah, nan mukayi wa Aunty B sallama zamu wuce gida, domin driver yana waje ummie ta turo yazo ɗaukan mu, haka muka fito gudu - gudu mukaje side ɗin amaryah muka gaisheta, tayi kyau tana sanye cikin wani lace black mai ratsin golden, fitted gown ne ya yi matuƙar amsan jikin ta, Gsky Aunty jeeddah tayi babu ƙarya ƴar gayu ce na nuwa, da fara'a sosai a fuskanta ta amshe mu, bayan mun gaisheta muka mata sallama zamu tafi, da sauri ta miƙe tana tmbyn meyasa bazamu zauna ba sai anjima? Da murmushi a fuskan mu nace mata ummie tace mudawo zamuyi aiki a gida, amma insha Allahu zamu zo, har bakin ƙofah ta rakamu hannunta na riƙe da hannuna, ina kallon hafsy sai harara na takeyi, ai kuwa muna shiga mota ta juyo tana harara na, " Adda wannan karon kan inaga sai Abba ys shiga lamarin mu, don babu yadda za'ayi ki ƙwace Aunty B, yanzu ma ki ƙwace Aunty jeeddah ba, duk iyayin ki sai kin bar mun ɗaya", ta faɗa tana wani tsuke baki da fuska, dariya muka kwashe da shi, ina riƙo ta jikina dama a gefe na take zaune, "haba hafsy masoyiya tah, ni dukkan su ma na bar miki, har mai zuwa a gaba ma, nidai fatana Allah ya bar mun ke, shine babban buri na," kwanciya tayi a kafaɗa na tana ƙyalƙyala dariya kaman ba ita bace take harara na yanzu, "Adda ae mai zuwa na gaban kai ae dama tawa ce, sai yadda nace", ta faɗa tana zungurin ummitah, mudai dariya muka musu.
Muna sauƙa a motan muka wuce side ɗin hjy ummah mu gaisheta, a parlor muka sameta dasu Aunty ma'u, Aunty Rakiya dasu yayah umar, gaishe su mukayi sannan na shige ɗaki na ajiye kayana.
Angama biki da 1week Yayah Mohd da yayah Ahmad suka fara shirin komawa Abuja, domin wannan karon yayah mohd zai tafi da Aunty B, sun kama gida wuri ɗaya da yayah Ahmad, gidan offstair ne ɗaya yana sama ɗaya yana ƙasa, ko wanne yana ɗauke 1 parlor 2 bedrooms, ana saura 2dys su tafi Abujan, Aunty b da Aunty jeeddah suka zo gida dukkan su suka wuni, ranan wani farin ciki na musamman nake gani a fuskan ummie, don lokacin ɗaura lunch tare muka shiga kitchen da su Aunty b, ummie dai tana zaune parlor da su yayah, don dukkan su ranan a parlon ta suka wani, akai - akai zakiga mamah ta shigo, abinci kala 2 akayi, domin ko wacce abinda mijinta yake so ta girka, suna ta raha a tsakanin su, nidai sai kallon su nakeyi ina jin daɗi a raina, nida hafsy da fatima aka barmu da haɗa drinks, mukayi zoɓo mukayi kunun aya, sannan hafsy ta sake haɗa tarmarrin juice, wai tasan shi yayah umar yake so, nidai kallon ta kawai nakeyi don nasan ƙarya ne, yayah umar kunun aya yake so shida yayah Ahmad, yayah mohd ne mai son zuɓo, yayah isgaq ne mai so, duk da ban ganshi a parlon ba amma nasan babu daɗewa zai zo, don inaga wataran a gidan nan ma yake wanka idan banyi ƙarya ba, haka muka je muka jera komai a ƙasan parlorn bayan mun shimfiɗa babban ledan cin abinci, domin ummi tace kada a ɗaura akan dinning
Suna dawowa a sallan azahar dukkansu suka shigo parlorn, murmushi nayi ganin harda yayah Ishaq, babu wani kunya ko takura na wani surkunta, ita ummie ta gaya musu su ɗauke ta uwa, itama ƴaƴa ta ɗauke su, ita dai bata son raini, amma duk abunda suke buƙata wanda uwace keyi tou bata ɗauke musu ba su tunkareta, kuma ko wani matsalah ne idan baifi ƙarfinta ba su sameta, bata son su nemi iyayen su sai sunga gazawanta, zuwan su sama sai da ta zaunar dasu da mazajen su ta musu nasiha sosai, sannan ta nemi haɗin kansu dasu zauna da junan su lafiya, kallon Aunty jeeddah tayi tace, "Hauwa maijeeddah, yanzu ne kika shigo cikin mu ke, domin ita Bintu ta riga da ta daɗe da shigowa, mun santa ta sanmu, domin ta zauna dani ɗaki ɗaya na tsawon shekara guda, yanzu kece kika shigo kuma bana so ki ɗauki kanki kaman baƙuwa, kema ki saka a ranki tuntuni kina tare a cikin mu, yanzu kece ƙarama kafin auta na ya kawo ta shi, abunda nake so dake kiyiwa Bintu biyayyah kamar kina tare da babbar yarki, ku haɗa kanku kada ku bada ƙofan da za'a shiga tsakanin ku, domin haɗin kanku shine ƙarin haɗin kan ƴaƴa na, ni kuma shine burina da nutsuwata, mu haɗa kai dukkan mu mu zama abu ɗaya, shine fata na da buri na, kuma dukkan ku irin so ɗaya nake muku, babu wacce tafi wata a wurina sai wacce tafi kyautata mun, kuma tafi zaman amana da mu, ni wacce umar na zai aura tun bata zo ba iri ɗaya nake jinku a zuciyata, yadda dukkansu ƴaƴan iri ɗaya nake jin su a raina, saidai wanda yafi kyautata mun" nasiha sosai ummie ta musu, kuma tayi wasu yayah ma, bayan fitan matan su ma ta ƙara yi musu, domin yadda muka taso da son junan mu tana so abun ya miƙe har kan ƴaƴa da jikoki, inda ta nuna musu haɗin kan matan su shine nasu haɗin kan, domin idan matan su babu haɗin kai zai shafi zumuncin su, don kowa nashi ya sani, haka dai aka zauna cin abincin kowa cike da farin ciki, filet ɗaya Aunty B ta zuba musu da Aunty jeeddah, nima da hafsy da fatima filet ɗaya muka zuba yadda muka saba ci da hafsy tare, yaya umar da yayah ishaq na nasu tare, yayah mohd da yayah Ahmad da ummie filet ɗaya suka zuba, domin yawan cin lokuta tare suke cin abinci, da ƙyar kiga ummie nacin abinci dani ko hafsy, amma yayah Ahmad da yayah mohd yawanci tana cin abinci tare da su, tun bama yayah mohd ba, shi yawan ci duk irin abunda ummie keso na abinci shima yana so, don ko zuwa yayi duk inɗa ta zauna yana gefenta, idan ta koma ɗaki zakiga baya wani daɗewa zai bita, idan tayi kitchen ma zaki ganshi ya bita, toilet ne kawai da bayida iko baya binta, kuma har yanzu idan ya zauna zakiga ya jingina da ita, narasa wani irin ƙulafucin uwa yake da shi a zuciyan shi, Areefh dai yana gefen yayah umar, don tunda suka zo yake wurin shi domin son shaƙu sosai.
Gaba ɗaya parlon ya ɗauki shiru, banda ƙaran spoons sai Areefh da yake ta gulaniyan shi, a haka mukaga an ɗago labulen parlon da sallama, Abba ne ya shigo, hannu ya saka ya riƙe haɓan shi yana duban mu ɗaya bayan ɗaya, idon shi ya tsayar akan ummie yace, "baiwar Allah irin wannan wariyar launin fata haka? Haba baiwar Allah ae sai aɗan taimakawa marayan Allah ɗan ɓoto a gayyace shi yazo shima ayi wannan ciye-ciyen da shi, kayan daɗi iya kayan daɗi amma sai a ware ni gefe guda"? Ya faɗa yana neman wurin zama a gefen yayah umar da yayah ishaq, mudai parlon gaba ɗaya dariya muke mishi, sannan kowa yana mishi sannu da shigowa, hararan su yayah mohd yayi yana cewa, "ni ae tunda naga muhammadu an fito a sallah bai wani tsaya munyi hiraba ya wani kamo hannun ɗan'uwan shi Ahmadu sukayi gaba har suna tuntuɓe na xargi wani abu, ubana ne kawai da ishaq suka ɗan tsaya da mummunan ɗansu muka ɗan zanta, a lokacin nace tou anya babu wani abu da ake ɓoye mun?".
Dariya ummie tayi tace, "wallahi kana raina, duk loma ɗaya idan nayi naji daɗin girkin da ƴaƴana suka shirya mun sai na tuno ka, kawai dai babu yadda zanyi ne na share, don nasan amaryah ta shiyah maka table da danasha", ta faɗa tana kallon shi da dariya, dukkan mu dariya mukayi ganin yadda Abba ya wani kama haɓa yana hararan ummie, kallon sa ya maida kan su Aunty b yace, "yanzu yarana hadda ku anuna mun wariya ko"? Sun kuyar da kai Aunty B tayi tana dariya, a hankali tace, "Abba nima fah kana raina shiyasa na zuba maka naka a flask, yana kitchen dama jira nakeyi muna gama na bawa hafsy ta kai maka", ta ƙarasa tana dariya.
Spoon yayah umar ya miƙawa Abba yana cewa, "rabu da kowa Abba muci abinci tare, kaga nima ware ni sukayi, dama kullum haka ake mun, shiyasa kaga sau ɗari wurinka ko wurin hajjaju makkatu nake zuwa ci, don yayah mohd yana shigowa yake cinye abincin gidan nan shida ummin shi," ya faɗa yana kai loman abinci bakin shi, dariya mukayi ummie tana cewa, "wallahi yaron nan kaji tsoron Allah, nafi yawan cin abinci da kai fah, yanzu ka fito da tsirfah kala -kala kace baka cin wannan baka cin wannan" haka dai akayi ta raha ana cin abincin, wanda Abba sai da yaci duka girki kala biyun yana ta santi, ana gama ci muka tattare komai, sannan Abba yaja ƴan mazan suka tafi side ɗin shi, mu kuma dukkan mu muka wuce wurin hajiya ummah, ummie kawai muka bari.
Wuraren ƙarfe 9:00 na dare suka yi shirin tafiya, lokacin yayah Mohd yake gayawa ummie Abba yace umar, ishaq, hafsy, raliya da ni zamu musu rakiya, da yake flight zamu bi sai yace zamuyi 1week mu taya su shiga sabon gida sai mudawo, gaba ɗaya muka ɗauki murna nida hafsy, ita ma fatima sai taji daɗi, domin dama har ta fara mitan ita kaɗai zataje ta dawo, don itama ta fara ATBU damu, tou anyi idan lokacin school ne zata zauna damu, idan anyi hutu sai ta wuce Abujan, haka muka rakasu wurin motocin su muna ta murna.
Washegari hafsy mukaji muryan mamie tana ta zabga masifa, da ta kwana biyu batayi ba, don tunda aka gama bikin nan batayi wani abun azo a gani ba, sai da hafsy ta fita ta jiyo don tsegumi, tazo tana gaya mana wai akan maganan komawan su yayah Abujah ne, wai Abba ya sake ƙarar da kuɗin shi wurin saya musu gida, ita bata yadda ba su ƴaƴa matan ba ƴaƴa bane? Nan Abba ya watse ta yace mata gida ba saya akayi ba, rent suka kama kuma kowa da kuɗin shi ya kama, amma haka ta dinga rantsuwa akan Abba ne yasaya, idan ma kamawan ne shi ya kama, kuma bazata yadda ba, shi kuma yace kada ta yadda ta kaishi ƙara koton ƙulin duniya, sannan tace kuma babu inda raliya zataje, kala taje a cutar mata da ƴa, yadda aka so cutar da habiba a mallake mata ƴa, a nan ne Abba yace mata ita taso shi ya gajji da fitinan ta, shi dai yayi ƙoƙarin haɗa kan ƴaƴan shi, amma tunda ita ta raba ita taso, itace da baƙin ciki gaba ba shi ba, nan mamie ta sake maimaita "raliya fah bazata je ba, kalan idan sun dawo kace suje gidan habiba? Wanda bansan wani sharrin za'a shiga mata da shi ba? Kowa yanzu ya tsaya kan nashi, don baza je a wargaza mun zaman lafiyan ƴa ba, ita kuma wannan da tauraron ta ke haskawa baza'a je a wargaza mata nata, domin an haɗa kai da mutanen borno ae babu abun da bazasu tsayawa mutum ba, anan ne mamah ta fito ta mata jan ido tukun ta koma ɗakin ta.
Murmushi ummie tayi tace ita dama bata saka aranta raliya za'a bar ta taje ba, saboda haka ita ta sani fitina kawai maganan zai jawo, Allah ya kyauta kawai ummi tace, mudai babu abinda ya dame mu shirin kayan mu kawai muka cigaba dayi, muna ciki shirin naga ƙiran M.G na shigowa wayana, kallon waya na tsaya yi ban ɗauka ba, don tun ranan da suka isa Abuja bai sake ƙirana ba, ban san kuma dalili ba.
*AUNTY NICE
managarciya