Home Rahoto An yi wa mutane 6 kisan gilla da jefa jariri rijiya a...

An yi wa mutane 6 kisan gilla da jefa jariri rijiya a Kano

4
0

Mutum shida aka yiwa kisan gilla a gidan wani bawan Allah mai suna Haruna Bashir da ke unguwar chiranchi a karamar hukumar Kumbotso.

Mai dakin sa Fadima ta rasa ranta taare da ‘ya ‘yan ta 6 wanda jariri biyu aka jefa cikin rijiya. Sai dai tuni aka garzaya da daya daga cikin yaran zuwa asibiti sakamakon motsi da aka ga yanayi.

Lamarin ana zargin ya faru da wannan safiya ta Asabar wanda kawo yanzu ba akai ga gano masu laifin ba, saidai ana kyautata zaton anyi amfani da tsani wajen shiga ko ficewa daga gidan yayin aikata dan yen aikin kamar yadda wakilin mu Ado Danladi Farin Gida ya rawaito.

Tuni jami’an yan sanda suka isa gidan dan tattara bayanai kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here