Wasu gungun Malamai a Kano sun ba da sanarwar sauke shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil daga mukaminsa, a cewarsu ya afkar da kingiyar cikin siyasa dumu dumu da kuma zargin sama da faɗi da kuɗin ƙungiya.
Haka kuma, Malaman na zargin Sheikh Khalil da yin fadan babu gaira babu dalili da Gwamnatin Kano karkashin Jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A saboda haka, Malaman suka bayar da sanarwar nada Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin sabon shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano.
Hakan ana yi tunananin sabon rikici ne ya kunno a tsakanin malaman Kano kan wasu dalilai da ba a bayyana ba.