An tsare Shuwagabannin Kananan Hukumomi 6 kan zargin karkatar da kudi a Kano
An tsare Shuwagabannin Kananan Hukumomi 6 kan zargin karkatar da kudi a Kano
Hukumar Yaki da Rashawa da kuma Karɓar Korafi ta Jiahr Kano (PCACC) ta tsare shugabannin ƙananan hukumomin ne bayan da suka amsa laifin karkatar da kuɗaɗen zuwa aljihunsu.
Shugabannin kananan hukumomin su ne, shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdulaziz Sulaiman, da na Bebeji, Basiru Abubakar da kuma takwaransu na Ƙaramar Hukumar Garko, Gambo Isa.
A halin yanzu dai suna can suna amsa tambayoyi a gaban jami’an binciken hukumar tare da wasu mutane 19.
Majiya: Rfi Hausa
managarciya