Wani sabon rahoto ya nuna cewa akwai yiwuwar Shugaba Bola Tinubu ya tura sunayen ministocinsa ga majalisar dattawa bayan ranar 4 ga watan Yulin 2023.
A satin da ya gabata, majalisar dattawa ta ɗage zamanta har zuwa ranar Talata, 4 ga watan Yuli, cewar rahoton The Guardian.
A lokacin da majalisar za ta ci gaba da zamanta, ana saran Shugaba Tinubu ya kammala haɗa sunayen ministocinsa domin miƙa wa a gaban majalisar ta tantance su.
'Yan siyasa na ci gaba da faɗi tashi domin ganin sun samu gurabe a cikin ministocin Shugaba Tinubu.
Gwamnoni da ke kan mulki, tsaffin gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ta kokawar ganin sun samu gurabe a cikin ministocin.
A cewar rahoton Vanguard, kamun ƙafar bai tsaya kawai a ƴan jam'yyar APC ba.
Jiga-jigan jam'iyyun adawa irinsu Peoples Democratic Party (PDP) da New Nigeria People's Party (NNPP) suma suna da muradin samun gurabe a cikin ministocin.
Fafutukar samun kujerar Ministan tarayya a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, ya jawo sabani tsakanin wasu cikin jagororin jam’iyyar APC.
Vanguard ta ce Gwamnoni da tsofaffin gwamnonin jihohi da shugabannin APC su na yaki domin ganin Bola Ahmed Tinubu ya ba su mukamin Minista.
Baya ga wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC, akwai kusoshin jam’iyyun adawa irinsu PDP da NNPP da ke harin Ministoci a gwamnati mai-ci.
Wasu majiyoyi sun ce sabon shugaban kasar zai aika da sunayen Ministocinsa zuwa majalisa a ranar 4 ga Yuli da Sanatoci za su koma bakin aikinsu.
A wani rahoton na daban, an fahimci za a rantsar da Ministoci ne bayan kammala shari’ar da ake yi a kotu a kan sakamakon zaben shugaban kasa.
A jihohi irinsu Osun, rikici ake yi tsakanin tsohon Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola da magajinsa Gboyega Oyetola da ya rasa tazarce a 2022. Sanannan abu ne ba a ga maciji tsakanin magoya bayan Abdullahi Umar Ganduje da Rabiu Kwakwanso wanda yake samun fada wajen shugaban kasa.
Wasu jagororin APC sun huro wuta cewa bai kamata shugaba Tinubu ya nada kowa ba sai cikakkun ‘yan jam’iyya da su taimaka masa a zaben 2023.
Wata majiya ta tabbatar da cewa ana ta karbar takardun CV na masu harin zama Ministoci, amma har yanzu an rasa gane inda shugaban kasa ya dosa.
A cewar wani na kusa da fadar, babu mamaki masu bada shawarar da aka nada su samu iko sosai a gwamnati, ya zama su ke juya Ministocin da za a nada.