An Nemi Bola Tinubu An Rasa Ana Tsakiyar Kamfe A Jihar Neja 

An Nemi Bola Tinubu An Rasa Ana Tsakiyar Kamfe A Jihar Neja 


Ba wani abin tashi hankali domin  Asiwaju Bola Tinubu ya bar filin kamfe a lokacin da ba a tashi ba, kamar yadda wasu suke kokarin nunawa. 

Punch ta ce Darektan yada labarai da hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a APC ya fitar da jawabi a kan abin da ya faru yau. 
A ranar Larabar nan, Bola Tinubu da shugabannin APC suka je Minna, jihar Neja domin kamfe. 
Hakan na zuwa ne bayan gangamin da aka yi a Kaduna. 
A jawabin Bayo Onanuga, ya musanya rade-radin cewa an dauke dan takaran na jam’iyyar APC daga taronsu da aka yi a Minna ne saboda rashin lafiyar da ta taso masa.