An Kaddamar Da Rabon Tallafin Gwamnatin  Kebbi Ga 'Yan Gudun Hijira Dake Zuru

An Kaddamar Da Rabon Tallafin Gwamnatin  Kebbi Ga 'Yan Gudun Hijira Dake Zuru
 

 

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

 

Gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta gabatar da tallafi ga yan gudun hijirar da rikicin yan ta'adda ya raba su da muhallansu a garin Zuru.

 
Shugaban karamar hukumar Zuru Hon Muhammad Bala Isah Gajere Skudu (TALBAN ZURU) shine ya kaddamar da rabon kayayyakin abinci ga yan gudun hijira a sansanin su da ke cikin Isgogo 
 
Bala Gajere ne da kansa ya mika wannan tallafin ga mutanen da suka koma Kauyukan nasu sakamakon samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a garuruwansu, 
 
Gwamnatin Jihar Kebbi tare da hadin gwiwar karamar hukumar Zuru sun ba da tallafin kayayyakin abinci inda gwamnan jihar Kebbi ya bayar da Shinkafa da kudade ga yan gudun hijirar,
 
Kana Hon Muhammad Bala Isah Gajere Skudu (TALBAN ZURU) shi ma haka ya bayar da buhu huwan abinci ga yan gudun hijirar, inda ya tallafa musu da buhuhuwan dawa da na masara a kashin kansa,
 
Bala Gajere ya jinjinawa Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu bisa gagarumin tallafin jin kai ga yan gudun hijirar Zuru,, 
 
Ya kaddamar da bikin raba kayan abinci tare da hadin kan masarautar Dabai da shugaban jam'iyyar APC Alh Aliyu Abubakar Abiola, tare da kansilolin karamar hukumar Zuru da darktoci,
 
Da yake kaddamar da shirin rabon da aka yi a sansanin yan gudun hijira na garin Isgogo Bala Gajere ya yi yaki da masu rabawa don tabbatar da karkatar da yan gudun hijirar da aka samu mafaka a sansanin,
 
Gajare ya nanata cewa Gwamnan jihar Kebbi yana cikin Gwamnonin da ke yaki da ta'addanci,
 
Bala Gajere ya ji dadin yan gudun hijirar da suka tashi tsaye wajen yi musu addu'o'in samun zaman lafiya da cigaba kuma da yardar Allah ya zaman lafiya yana dada samuwa acikin wannan yankin.