An Gudanar da addu'ar rokon Ruwa a Zamfara

An Gudanar da addu'ar rokon Ruwa a Zamfara
An Gudanar da Sallar rokon Ruwa a karamar hukumar Kaura Namoda jihar Zamfara bayan shafe kwanaki da dama babu Ruwan Sama.
 Mutane da dama hankulansu ya fara tashi duba da cewar kwanakin  damina sun jima da tsayuwa amma har yanzu shiru ba wadatar ruwa a yankin.
 Yayin da wasu mutanen iraruwansu na cikin ƙwarya domin jiran ruwan shukar amma har zuwa ranar Laraba ta wannan satin da suka fita rokon ruwa.
Babban limamen garin Kaura Liman Malam Badamasi ne ya jagoranci Sallar rokon ruwan tare da nuna bukatar yin hakan ganin an yi mako biyu ba a samu ruwa a garin ba.
Sheikh Malam Muhammad na gangaren Makaranta ya gabatarda nasihohi masu ratsa zukata akan Muhimman lamura dake kawowa fadawa acikin waɗannan musifu na ɗaukewar ruwan sama da kuma ibada daya kamata a yawaita yi  adaidai wannan lokaci domin gushewar Wannan farin da ake ciki.
Abdul Hadi Ibrahim Mai yadi  da Ƙasimu Namadi na daga cikin wadanda suka samu halartar Masallacin suma sun nuna damuwarsa da kuma ƙasantar da kawunansau ga Ubangiji domin neman yafiya akan dukkanin zunubansu ko Allah zai shayar damu akan wannan lamari.
Abdul Hadi Ibrahim Mai yadi  da Ƙasimu Namadi na daga cikin wadanda suka samu halartar Masallacin suma sun nuna damuwarsu da kuma ƙasantar da kawunansau ga Ubangiji domin neman yafiya akan dukkanin zunubansu ko Allah zai shayar da su akan wannan lamari na fari.
Sun ce yanzu mako biyu kenan ba su ga ruwa a yankinsu ba, ruwan da suka samu ba su wadaci shuka ba sai gashi sun dauke gaba daya, gashi kuma ana ana cikin Damina sosai amma ba ruwan shuka.
"Fari na Ruwa abin tashin hankali ne ga duk wani mai hankali ko shi ba manomi ba ne, wannan musiba ce da ya kamata kowa ya tashi tsaye a duk in da yake ya roki Allah ya ye wannan musibar ta karancin ruwan sama," a cewar su.