Matakin na zuwa ne gabanin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na shekarar 2027 a Kaduna, inda aka jibge jami’an tsaro a muhimman wurare daban-daban na birnin domin hana yiwuwar lalata kayan tallan yakin neman zaben.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa daga cikin jami’an da aka sanya aikin kare fastoci da allunan tallan akwai na Hukumar KASTLEA mai kula da bin dokokin zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kaduna da kuma Jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Nijeriya NSCDC.
An fi mayar da jami’an ne kan manyan hanyoyin da suka doshi filin wasa na Kaduna Township Stadium, inda ake sa ran gudanar da gangamin yakin neman zaben.





