An fara mancewa da mutanen jami’ar Gusau dake hannun ‘yan bindiga
A lokacin da aka sace dalibban da ake zargi yawansu ya kai 30 duk da har yanzu a hukumace ba a sanar da yawan dalibban da ‘yan bindigar suka tafi da su ba, Gwamna Zamfara, Dauda Lawal ya kira taron gaggawa na Majalisar Tsaron Jiha.

Harin ‘yan bindiga a yankin Arewa maso yamma musamman Sakkwato Zamfara da Katsina da Kaduna ya zama wani abu da ake kira Karin kumallo domin sama da shekara 9 a yau ba wata rana da ba za a kai harin ta’addacin a daya daga cikin jihohin ba.
‘Yan gudun hijira da suka bar jihohin, har yanzu ba wata hukuma da ta fayyace adadin yawan mutanen ko kuma yawan dabbobi da abincin da aka yi hasara tun sanda aka sanya yankin a cikin matsalar tsaro ta ‘yan bindigar sunkuru.
‘Yan bindiga sun sake addabar yankin Arewa bayan dogon shiru da aka samu bayan kammala babban zaben kasa har zuwa bayar da mulki ga wadanda suka yi nasara, ba ji ba gani sun dawo da kai hari sosai, na baya-baya nan mafi muni da suka yi daukar mata ‘yan makaranta a jami’ar tarayya ta Gusau da kai hari a kananan hukumomin Goronyo da Binji a Sakkwato, hakan ya sanya wasu al'mma a jihar sun fara kare kansu daga harin 'yan bindigar.
A lokacin da aka sace dalibban da ake zargi yawansu ya kai 30 duk da har yanzu a hukumace ba a sanar da yawan dalibban da ‘yan bindigar suka tafi da su ba, Gwamna Zamfara, Dauda Lawal ya kira taron gaggawa na Majalisar Tsaron Jiha.
An sace su ne a muhallinsu dake wajen jami’a, a kauyen Sabon Gida na ƙaramar hukumar Bungudu.
A sanarwar manema labarai, wadda mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ya ce an kira taron gaggawan ne domin tabbatar da ganin an ceto dukkanin waɗanda aka sace, tare kuma da bin hanyoyin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar Zamfara.
Ya ƙara da cewa, Gwamna ya ba mataimakinsa Mani Mallam Mummuni umarnin jagorantar taron na majalisar tsaro.
Ya ce: “A yayin wannan taro, shugabannin ɓangarorin tsaron na Zamfara sun tabbatarwa da mataimakin gwamnan ƙudurinsu na wanzar da zaman lafiya. Sun kuma shaidawa mataimakin gwamnan cewa sun samu nasarar ceto mutum Shida cikin waɗanda aka sace.
“Sun ƙara ƙara da cewa, jami’an tsaro sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga da dama cikin waɗanda suka saci ɗaliban, inda kuma suke ci gaba da bin sahun ragowar.
“Mani Mallam Mummuni ya ja hankalin shugabannin tsaron da su ƙara tsananta sintirin jami’an tsaro a wuraren da aka san suna da hatsari.
“Daga ƙarshe mataimakin gwamnan ya jaddada wa al’umman Jihar Zamfara cewa gwamnati da jami’an tsaro ba za su yi ƙasa a gwiwa ba, har sai an shawo kan wannan matsala.”
A yanzu tun bayan ceto Karin wasu dalibbai 16 ba a sake jin maganar dalibban daga hukumomin tsaro ko wadanda ke rike da yaran ba, abin da wasu ke ganin kamar an fara fita batun sauran wadan da ke hannu domin rashin gatan da suke da shi.
Sace dalibban ya haifar da cece-ku ce tsakanin gwamnatin tarayya da Gwamna Dauda Lawal in da ya ce Gwamnatin Zamfara tana da gamsassun hujjoji da ke fallasa wasu jami’an Gwamnatin Tarayya da hannu a shirya zaman sulhu da ‘yan bindiga.
Bayan da Ministan yada Labarai da Wayar da kai, Alhaji Mohammed Idris ya zargi Gwamnatin Zamfara da siyasantar da lamarin tsaro, bayan neman ƙarin bayani da Gwamna Dauda ya yi kan zargin zaman sulhu ta ƙarƙashin ƙasa da ‘yan bindiga.
A takardar manema labarai, mai magana da yawun gwamnan Zamfara, ya bayyana cewa gwamnatin Dauda Lawal tana da hujjoji masu tada hankali da ke fallasa wasu jami’an Gwamnatin Tarayya kan sulhu da ‘yan bindiga.
Ya ƙara da cewa Ministan na Labarai ya yi ri-ga mallam masallaci wurin yanke hukunci tare da yankewa gwamnatin Zamfara hanzari.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mun nemi ƙarin bayani daga Gwamnatin Tarayya kan zaman sirri na sulhu da wasu jami’anta suke jagoranta a Zamfara ba tare da sanin Gwamnatin Jiha ko shugabanni jami’an tsaron jihar ba.
“Muna da gamsassun hujjoji dake tabbatar da wannan zaman sulhu tsakanin jami’an Gwamnatin Tarayya da ‘yan bindiga a wurare mabambanta a Zamfara.
“Ba mu san daga inda Ministan ya samu ƙwarin gwiwan bugun ƙirji ya ce babu wani zaman sulhu da aka yi a Zamfara ba, saboda ai mun bayyana wuraren da aka yi waɗannan zama, irinsu Birnin Magaji, Maradun, Mun Haye, Ajah, Bawo, da kuma Bagege.
“Muna sake nanatawa cewa sulhu da ‘yan bindiga a Zamfara ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba. Sam! Ba wannan ba ne mafita ga matsalar, a yi amfani da karfi kawai a kauda su, wanna ita ce matsayarmu har gobe.
“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta daina biye wa ‘yan amshin Shata, ta yi bincike tare da wanke kanta daga aikin waɗannan dillalan sulhu da ‘yan bindiga.”
An fara mantawa da yaran tun bayan da aka sace su wasu na dauka ma yaran sun dawo a hannun iyayensu ganin yanda aka fita batun maganar gaba daya.
A satin nan da ya gabata uwar gwamnan Zamfara Hajiya Huriya Daidai Lawal ta Kai ziyarar jaje a jami'ar kan sace yaran da aka a yi a watan da ya gabata.
Ta nuna bacin ranta sosai kan faruwar lamarin ga 'yan uwa mata Kuma ta ce za su yi kokari a kwato su da tabbatar da hakan bai sake faruwar ba.
Maganar da ake yadawa kan cewar Bello Turji ya sake dawowa ruwa waton yin Garkuwa da mutane Malam Bashir Guyawa yace baya da masaniya kan wannan “Turji yaransa ba su zuwa ko’ina, ba ka zuwa kai kudin fansa a wurinsa, wadanda ke addabar mutane a yanzu yaransa ne da yaye ya baiwa makamai, ya bar fita ba wata barazana da ta fito daga wurinsa kuma bai ce ya aje makamai ba sai dai ya daina Garkuwa da mutane a yanzu.
"Maganar tsaro ba da gaske ake yi ba tun da har aka baiwa 'yan siyasa damar su gyara motar yaki da kansu, yaushe za a magance matsala, an kasa yin abin da ya dace" Bashir Guyawa Isa.