An Bukaci 'Ya'yan Jam'iyyar APC A  Kebbi Da Su Kasance Masu Biyayya Ga Dokokin Jam'iyya

An Bukaci 'Ya'yan Jam'iyyar APC A  Kebbi Da Su Kasance Masu Biyayya Ga Dokokin Jam'iyya
 
Daga Abbakar Aleeyu Anache, 
 
Zababben shugaban Jam'iyyar APC a karamar hukumar mulki Zuru a karkashin jagorancin Alh Abubakar Abiyola ya bukaci ya'yan jam'iyyar All Progressives Congress APC da su kasance masu biyayya ga dokokin jam'iyyar,
 
Abiyola ya kuma yabawa ya'yan jam'iyyar APC bisa kokarin da suka nuna wajen gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka gudanar a matakin kasa, 
 
Shugaban jam'iyyar APC Alh Abubakar Abiyola ya cigaba da cewa ina kara jaddada goyon bayana tare da al'ummar da ke tare dani akan tafiyar gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu kuma ya zama wajibi mubi duk wani mai ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a matakin kasa da jihar Kebbi dama kananan hukumomi,
 
Alh Abubakar Abiyola ya bayyana hakan ne a ofishin jam'iyyar APC da ke acikin garin Zuru inda yake bayyana aniyarsa tare da nuna goyon bayansa ga gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu,