An bukaci kotu da ta dakatar da bikin rantsar da Tinubu tare da tsawaita wa'adin Buhari

Wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja sun bukaci wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta dakatar da bikin rantsar da zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Mazaunan da su ka haɗa da Anyaegbunam Ubaka Okoye, David Aondover Adzer, Jeffrey Oheobeh Ucheh, Osang Paul da Chibuke Nwachukwu su ka wakilta su na neman kotu ta haramtawa Alkalin Alkalan Najeriya da duk wani jami’in shari’a da/ko wata hukuma ko wasu mutane rantsar da kowane dan takara na zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Fabrairu a matsayin shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa.
Sun ce an yi hakan ne domin shari'a ta yanke hukunci daidai da tanadin sashe na 134(2) (b) na kundin tsarin mulkin Najeriya, cewa dole sai wannan dan takarar ya cika sharuddan tsarin mulki.
Su na kuma son umarnin kotu na ware ko dakatar da duk wata sanarwa ko bayar da takardar shaidar lashe zaben ga duk wani dan takara a zaben shugaban kasar na ranar 25 ga watan Fabrairu ko kuma an zabe shi sai dai idan shari’a ta yanke hukuncin karshe kuma sai wannan ɗan takarar ya cika sharuddan da aka bayyana a Sashe na 134 (2) (b) na Kundin Tsarin Mulki.”
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta bayyana Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour, wadanda suka zo na biyu da na uku, suna kalubalantar nasarar Tinubu a kotu.