Amfanin Ganyen Yaɗiya Ga Mata

Tana maganin Ciwon Mara wanda mata da yawa ke fama da shi.

Amfanin Ganyen Yaɗiya Ga Mata

Amfanin Ganyen Yaɗiya Ga Mata

*Daga Maryam Ibrahim.*


Ƴar uwa shin ko kinsan amfanin Ganyen Yaɗiya?

*Yaɗiya* waƴansu sun ɗauketa ne kawai abin Ƙwaɗawa da Yaji da kayan ɗanɗano aci.

To ba'a nan kaɗai ne hanyar sarrafa *Yaɗiya* ba.

Za ki iya sarrafata ta hanyar dafata tare da jarr kanwa ƴar kaɗan. Ki tace ki dinga sha. Tana maganin Ciwon Mara wanda mata da yawa ke fama da shi. In sha Allah idan kika gwada wannan zaki ga amfanin hakan.

Ba'a nan kaɗai ne hanyar samun lafiya a jikin iccen *Yaɗiya* ba.

Ki dafata tamkar yadda kike dafata idan za ki yi kwaɗonta. Tana maganin Ciwon Lala da yara suke fama da shi.

Sai angwada....!