Ambaliya: 'Yan Siyasa Biyu a Sokoto Sun Tallafawa Mutanen Borno da Kayan Abinci na Sama da  Miliyan 30

Jarman Sakkwato da Abdulkadir Dan iyan jarma, sun Tallafawa Al-ummar Maiduguri da Tallafin kayan  Abinchi  na sama da  Naira Miliyan 30. 

Ambaliya: 'Yan Siyasa Biyu a Sokoto Sun Tallafawa Mutanen Borno da Kayan Abinci na Sama da  Miliyan 30
 
Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.   
                       
Sanannen Dan kasuwa kuma dan siyasa  a jihar Sokoto, Jarman Sakkwato Dakta  Ummarun Kwabo A.A ( Uban Marayu) tare da na Hannun Daman shi  Alhaji Murtala Abdulkadir Dan iyan Jarma, Sun ba da na su Tallafin kayan Abinchi ga Alummar Borno da ambaliyar Ruwa ta shafa kwanan baya.
Da yake Hannunta kayan A Fadar Shehun Borno, Dakta Abubakar ibn Umar Garba El-kanemi,  Sadaukin Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki, kuma Shugaban Hukumar Zakka da wakafi ta jihar,  ya bayyana cewa sakon ya  hada da kayan Abinchi; 
1.Buhuhuwan Shinka Mai nauyin kilo 100 guda 100 
2. Buhuhuwan Gari mai nauyin kilo 100 guda 100 
3. Katon na Taliyar Spagetting guda 100
4. Maggi Katon guda 100 da 
5. Jalkar Mai Guda 30
A lokacin hannun ta kayan a fadar Maimartaba Shehun Borno,  angabatar da addu'a ta musamman ga wadanda suka bayar da kayan da kuma godiya a Madadin Gwamnatin jihar da masarautar da daukacin Alummar Borno.