Almajirai: Ba Mutanen Sakkwato Ke Yin Bara A Birnin Jiha---Honarabul Mani Maishinko Katami
Da farko shugaban majalisar Malamai na kungiyar jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’ikamatus Sunna dake da hidikwata a birnin Jos reshen Sakkwato Shaikh Abubakar Usman Mabera ya godewa gwamnatin jiha kan gundunmuwar da suka bayar mafi tsoka da yawa ta miliyan 15 wanda hakan shi ne karon farko da suka samu taimako mafi tsoka a gwamnati duk shekarun da suka kwashe suna yin gidauniya a duk shekara. “A wannan shekara mun samu gagarumar nasara yin Allah ne a wannan shekara zamu tura malamai 555 a wurare daban daban cikin fadin jiha don gudanar da tafsirin azumi zamu saye motocin wa’azi da yin taron karawa juna sani da bukin musabakar kur’ani da sauran muhimman abubuwa da ke iya tasowa a wannan shekara, duk wani mutum da ya taimakawa wannan tafiya da kudi ko ilmi ko lokaci muna godiya gare shi Allah ya fi mu yabawa” a Cewar Mabera.
Honarabul Mani Maishinko Katami a lokacin yana Kwamishinan lamurran addini na jihar Sakkwato ya bayyana mutanen da ke yawon bara lungu da sakon birnin jihar baki ne da ke shigowa daga makwabtan jihohin Sakkwato da wasu kasashe da suke makwabtaka da su, ba ‘yan asalin Sakkwaton ba ne ke wannan yawon bara da wasu suka mayar amtsayin sana’a lamarin da ke ci ma al’umma tuwo a kwarya.
Ya yi wadannan kalaman ne a wurin bukin kaddamar da gidauniyar gudunmuwa ta ayyukkan raya ilmi da kayan wa’azi na Kungiyar Izala mai cibiya a birnin Jos a satin da yagabata dake harabar filin masallacin rokon ruwa a titin Sarki Yahaya ya ce ‘Maganar bara ba al’ummar Sakkwato ne ba kuma bamu da karfin da muke yin dokar hana wani dan wata jiha ya zo nan, kan haka mun yi kokarinmu na bayar da tallafi maras karfi da marayu da taimakon sallah duk wani mai adalci zai gode wa Allah kan ayyukkan da Matawalle ke yi na raya jiha.’ A cewar Katami.
Da farko shugaban majalisar Malamai na kungiyar jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’ikamatus Sunna dake da hidikwata a birnin Jos reshen Sakkwato Shaikh Abubakar Usman Mabera ya godewa gwamnatin jiha kan gundunmuwar da suka bayar mafi tsoka da yawa ta miliyan 15 wanda hakan shi ne karon farko da suka samu taimako mafi tsoka a gwamnati duk shekarun da suka kwashe suna yin gidauniya a duk shekara. “A wannan shekara mun samu gagarumar nasara yin Allah ne a wannan shekara zamu tura malamai 555 a wurare daban daban cikin fadin jiha don gudanar da tafsirin azumi zamu saye motocin wa’azi da yin taron karawa juna sani da bukin musabakar kur’ani da sauran muhimman abubuwa da ke iya tasowa a wannan shekara, duk wani mutum da ya taimakawa wannan tafiya da kudi ko ilmi ko lokaci muna godiya gare shi Allah ya fi mu yabawa” a Cewar Mabera.
Gidauniyar ta cika ta batse domin an samu fiye da abin da ake nema na naira miliyan 25 da dubu 500, gwamnatin Sakkwato ce ta ba da taimako mafi tsoka sai babban mai kaddamarwa Abdussamad Dasuki da ya ba da miliyan biyu kungiyar reshen kananan hukumomi sun hada milyan biyu da dubu 800.
managarciya