Albashi wata 11: ma'aikatan Asibiti sun yi zanga-zanga a Zamfara

Albashi wata 11: ma'aikatan Asibiti sun yi zanga-zanga a Zamfara

Ma'aikata da yawan gaske da suka hada da masu gadi da masu tsaftace wuri a Asibiti Yariman Bakura dake garin Gusau jihar Zamfara ne suka gudanar da zanga-zangar lumana kan rashin biyansu albashinsu na watanni 11 a Litinin data gabata.

Masu gadi da masu samar da tsafa suna  karkashin Wasu  Kamfunna Masu zaman kansa da ake kira Taula Security Guards da AIB Cleaners, sun rufe ko'ina a cikin Asibiti tun daga kofar shiga yayin zanga-zangar.
Manema labarai sun fahimci shugaban Asibiti da maras lafiya da ma'aikata an barsu a tsaye ba makama.
Mataimakin sufabaiza na masu gadi Alhaji Abubakar Abubakar ya ce suna zanga-zangar ne domin neman mafita saboda an rike masu albashi ne kusan  shekara daya kenan yanzu wata 11.
"Ina da yara shidda dana haifa babu albashi dole ne na nemi wata hanya don ciyar da su, bana karbar dubu 15 albashi na a wata tsawon wata 11, hakan da yawan magidanta suke Shan bakar wahala.
Wakilin kamfanin tsafta na AIB Alhaji Babangida Mainasara ya ce Kamfani ya yi korafi ga gwamnati da Asibiti kan albashin amma har yanzu ba a saurare su ba.
Kwamishinan 'yansandan Zamfara Muhammad Shehu Dalijan ya yi jawabi ga masu zanga-zangar tare da alkawalin zai bibiyi lamarin, don haka su bari a cigaba da aiki a Asibiti, za a gyara lamarin.