Akwai bukatar Samar da cibiyar tunawa da Margayiya AISHA LEMU

Akwai bukatar Samar da cibiyar tunawa da Margayiya AISHA LEMU

AKWAI BUKATAR SAMAR DA CIBIYAR TUNAWA DA MARGAYIYA AISHA LEMU

Mujallar Managarciya  ta samu labarin rasuwar margayiya Hajiya Bridget Aisha Lemu, mata ga sanannen malamin addinin Musuluncinnan na Najeriya, Margayi Shaikh Ahmad Lemu, a matsayin abin bakinciki da damuwa; amma ba abin da mutum zai yi da ya wuce addu’ar Allah gafarta mata.

Marigayiyar, wacce shahararriyar marubuciya ce, haifaffiyar kasar Ingila ce, wadda ta musulunta a shekarar 1961. Ta yi ayyukka sosai kan musulmi da Musulunci, wadanda da ba za a iya lissafa su ba, kwararriya ce kan ilmin addinin Musulunci, wadda ta koyar da dalibai a wurare daban-daban, wadanda suka hada da na Makarantar Koyon Larabci(SAS),  ita ce shugabar makaranta ta farko (wato principal) ta Kwalejin ‘Yan mata ta Sakkwato, (GGC Sokoto). Wadannan kadan ne daga cikin gagarumar gudummowar yada addinin Musulunci da ta bayar.  Ita ce ta kafa Tarayyar Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (wato FOMWAN), ta kuma tallafa wa mijin nata, wato Sheikh Ahmad Lemu wajen kafa Cibiyar Yada Addinin Musulunci wato Islamic Education Trust (IET).  Aisha Lemu mawallafiya ce mai basira, malama, masaniyar ilmin addinin Musulunci.  

Abin da ya mayar da ita daban a cikin tsaranta na wannan lokacin shi ne, damar da ta yi amfani da ita a wajen rubutu, har ta iya wallafa littafai masu dimbin yawa kan fannoni daban-daban na ilmin addinin Musulunci. Har yanzu, wadannan  littafan nata, suna a gaba-gaba wajen koyar da daliban makarantun Sakandare.

A rayuwarta ta duniya, ta sadaukar da mafiyawan lokutanta ga abubuwa masu kyau  na daukaka addini. Wannan ya ba ta damar fitowa da sabuwar manhaja kan ilmin addinin Musulunci, ya kuma kara daga sunanta wajen shiga a mafiyawan gidajen Nijeriya.

rokon Allah Ya gafarta mata, da mijinta  Ya sa sun  huta, Ya kuma sa hidimar da ta yi wa addinin Musulunci ta zama haske a kabarinta da kuma sanadin shigar ta Aljanna. Allah Ya baiwa iyalansu da jama’ar musulmi hakurin wannan babban rashi. Amin.     

Ta la’akari da irin wannan gagarumar gudunmuwar da wannan mashahuriyar boyar Allah ta bayar a cigaban addini da kuma gwagwarmayar da ta yi don cin nasarar hakan ne Managarciya ke ganin ya dace a samar da wata cibiya don tunawa da marigayiya Aisha Lemu.